Filato: Jam'iyyar PDP Ta Samu Gagarumar Nasara kan APC a Zaben Kananan Hukumomi

Filato: Jam'iyyar PDP Ta Samu Gagarumar Nasara kan APC a Zaben Kananan Hukumomi

  • Hukumar zabe mai zamna kanta ta jihar Filato ta fara bayyana sakamakon zaben kananan hukumomin jihar da aka gudanar ranar Laraba
  • A ranar Alhamis, shugaban hukumar, Plangji Cishak ya ayyana jam'iyyar PDP a matsayin wadda ta lashe kananan hukumomi 10 a zaben
  • Shugaban hukumar ya ce akwai sauran kananan hukumomi 7 da ba a kai ga bayyana sakamakon zaben nasu ba, wanda a yanzu kowa ke jira

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Filato - Jam'iyyar PDP ta samu gagarumar nasara kan APC da sauran jam'iyyun adawa a zaben kananan hukumomin jihar Filato da aka gudanar Laraba.

Jam’iyyar PDP ta samu nasarar lashe kujerun kananan hukumomi 10 yayin da hukumar zaben Filato (PSIEC) ta fara bayyana sakamakon zaben.

Kara karanta wannan

An gano yadda aka ba APC nasara bayan yarjejeniya da gwamnam PDP ya yi da Akpabio

Hukumar zabe ta fara sanar da sakamakon zaben kananan hukumomin jihar Filato
PDP ta lashe kananan hukumomi 10 yayin da aka fara fadin sakamakon zaben ciyamomin Filato. Hoto: @CalebMutfwang
Asali: Twitter

PSIEC ta fadi sakamakon zaben ciyamomi

Shugaban PSIEC kuma jami’in tattara sakamakon zaben kananan hukumomi 17 na jihar, Plangji Cishak ne ya bayyana sakamakon a ranar Alhamis, inji rahoton The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ce har yanzu hukumar na ci gaba da bayyana sakamakon zaben a hedikwatarta da ke Jos, babban birnin jihar ta Filato.

A cewar Plangji Cishak, har yanzu ba a bayyana sakamakon kananan hukumomi bakwai da suka yi saura ba.

Jam'iyyar PDP ta lashe kujeru 10 a Filato

Jam’iyyar PDP mai rike da madafun iko a jihar Filato, yanzu ta lashe kananan hukumomi 10 kamar haka:

  1. Barkin Ladi
  2. Mikang
  3. Shendam
  4. Bassa
  5. Riyom
  6. Jos ta Kudu
  7. Jos ta Gabas
  8. Kanam
  9. Qua’an Pan
  10. Langtang ta Kudu

Kananan hukumomi 7 da suka rage

Ga jerin kananan hukumomi 7 da ba a kai ga bayyana sakamakon zabensu ba:

Kara karanta wannan

Kananan hukumomi: Majalisar Dattawa ta shiga ganawar sirri kan matakin gwamnoni

  1. Pankshin
  2. Mangu
  3. Wase
  4. Jos ta Arewa
  5. Kanke
  6. Bokkos
  7. Langtang ta Arewa

Zaben ya gudana ne a dukkanin kananan hukumomi 17 da kuma gundumomi sama da 300 na jihar.

Filato: Masu kada kuri'a sun fusata

A wani labarin, mun ruwaito cewa masu kada kuri’a a jihar Filato sun bayyana rashin jin dadinsu kan yadda aka rika neman jami'an zaben jihar aka rasa a ranar kada kuri'a.

Rahotanni sun bayyana cewa an samu rashin halartar jami’an zabe na wucin gadi daga hukumar INEC a karamar hukumar Jos ta Arewa wanda ya kawo tsaiko wajen fara kada kuri'a.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.