'Siyasa ce', Kungiyar MURIC Ta Magantu kan Zargin Sanatan Arewa da Hannu a Ta'addanci
- Kungiyar MURIC ta yi Allah wadai da zargin Sanata Shehu Buba da ake yi da ɗaukar nauyin ta'addanci a Najeriya
- Kungiyar kare hakkin Musulmai ta ce babu hujjoji kan zargin sanatan wanda ya kasance haziki da ke hidimtawa al'ummarsa
- Hakan ya biyo bayan zargin da gwamnatin jihar Bauchi ta yi kan sanatan da daukar nauyin dan ta'adda zuwa aikin hajji
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Ƙungiyar kare hakkin Musulmai (MURIC) ta yi magana kan zargin Sanata Shehu Buba game da ta'addanci.
Kungiyar ta ce babu kamshin gaskiya kan zargin Sanatan Bauchi ta Kudu da ake yi duk siyasa ce kawai.
Ta'addanci: Kungiyar MURIC ta kare Sanata
Shugaban kungiyar, Farfesa Ishaq Akintola shi ya bayyana haka a jiya Laraba 9 ga watan Oktoban 2024, cewar rahoton Premium Times.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Akintola ya ce kwata-kwata babu wata hujja mai karfi kan zargin Sanatan da ake yi game da ɗaukar nauyin ta'addanci.
Farfesan ya ce abin takaici ne yadda Gwamna Bala Mohammed ke neman bata sunan Sanatan saboda siyasa kawai.
MURIC ta fadi alherin Sanata Shehu Buba
"Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya rubuta korafi kan zargin Sanata Shehu Buba da daukar nauyin ta'addanci."
"Wannan zargi babu kamshin gaskiya kuma shaci-fadi ne da babu gamsassun hujjoji."
"Gwamnan ya zargi Sanata mai kokari ga al'ummarsa domin bambancin siyasa inda yake zarginsa da aikata laifi mafi girma a Najeriya."
- Farfesa Ishaq Akintola
MURIC ta bukaci a binciki makarkashiya da Gwamna Bala ke shiryawa inda ta ce mafi yawan gwamnoni da ke wa'adinsu na karshe na neman kasancewa da karfin iko har bayan barin ofis.
An zargi Sanata da daukar nauyin ta'addanci
Kun ji cewa Jami'an DSS sun fara binciken Sanata Shehu Buba bisa zargin alaka da wani rikakken dan ta'adda Abubakar Idris.
An gano alamun alaka tsakanin Sanatan da Abubakar bayan hadiminsa Yahaya Ibrahim ya biyawa dan ta'addan aikin hajji.
Zuwa yanzu, an cafke Abubakar Idris, sannan kuma DSS ta mika rahoto kan Sanata Shehu Buba ga shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng