Kotu Ta Tumɓuke Dan Majalisar Wakilai, Ta Tono Maguɗin Zaɓe da PDP Ta Yi

Kotu Ta Tumɓuke Dan Majalisar Wakilai, Ta Tono Maguɗin Zaɓe da PDP Ta Yi

  • Kotun daukaka kara a jihar Enugu ta tumɓuke dan majalisar wakilai na jam'iyyar PDP kan karar da wanda ya kalubalance shi ya shigar
  • Kotun ta bayyana cewa an yi magudi yayin zaben kuma akwai kuskure wajen sanar da cewa shi ya samu kuri'u mafi rinjaye a takarar
  • A yanzu haka dai kotun ta yi umarni da a kwace shaidar cin zabe da hukumar INEC ta ba shi a mika ta ga dan takarar jam'iyyar LP

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Enugu - Jam'iyyar PDP ta rasa dan majalisar wakilai bayan kotun daukaka kara ta yanke hukunci a jihar Enugu.

A yau Laraba ne kotun ta tabbatar da soke nasarar da dan majalisar wakilai, Hon. Simon Atigwe ya samu yayin zaben da aka yi a 2024.

Kara karanta wannan

Atiku ko Wike? Shugabanni sun bayyana wanda ya haddasa rikicin da ya mamaye PDP

Kotun tarayya
Kotu ta rusa zaben dan majalisar wakilai. Hoto: Kola Sulaimon
Asali: Getty Images

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa kotun ta ba dan takarar LP nasara wanda shi aka fara sanarwa ya lashe zaben a 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda dan LP ya samu nasara a majalisa

A karon farko, dan takarar LP Hon. Dennis Nnamdi Agbo ya ci zaben dan majalisar wakilai a shekarar 2023.

Bayan shigar da korafi, an rusa zaben inda aka sake wani zabe a shekarar 2024 kuma ɗan PDP ya samu nasara aka rantsar da shi.

Kotu da tumɓuke dan majalisar wakilai

Biyo bayan shigar da karar da dan LP ya yi, a yau Laraba kotun daukaka kara a Enugu ta rusa nasarar da dan PDP ya samu a zaben 2024.

Premium Times ta ce kotun ta bayyana cewa an yi aringizon kuri'u a zaben kuma ɗan PDP bai ci zaben ba kwata kwata.

Kara karanta wannan

Abubuwa 3 da suka jawo karamar jami'yya ta buga APC da PDP a kasa a Rivers

Alkallin kotun, mai shari'a H N Kunaza ya ce dan PDP ya samu kuri'u 21,863 shi kuma ɗan LP da ya yi nasara ya samu kuri'u 23,221.

Wani umarni Kotun daukaka kara ta ba INEC?

Biyo bayan hukuncin, kotun daukaka kara ta umarci hukumar INEC ta karbi shaidar cin zabe da ta ba dan takarar PDP, Simon Atigwe.

Haka zalika kotun ta tabbatar da cewa za a ba dan takarar LP, Dennis Nnamdi Agbo shaidar cin zabe kuma a rantsar da shi.

Wike ya fadi dalilin kayar da PDP a 2023

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Rivers kuma ministan Abuja, ya yi magana kan zaben shugaban kasar da ya wuce.

Nyesom Ezonwo Wike ya ce bai yi nadama ba a kan yadda ya juya baya ga tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar a 2023.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng