"Ba Komai Za Ka Yi Nasara ba": Gwamna ga Minista, Ya Fadi Silar Rikici Tsakaninsu

"Ba Komai Za Ka Yi Nasara ba": Gwamna ga Minista, Ya Fadi Silar Rikici Tsakaninsu

  • Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara ya roki Ministan Abuja, Nyesom Wike da ya bar rigimar siyasarsu ta zama tarihi
  • Mai girma gwamna ya ce bai kamata tsohon gwamnan ya ce sai ya yi nasara kan dukan fadan da ya ke yi ba musamman a jihar
  • Fubara ya fadi musabbabin fadan da ke gudana tsakaninsa da mai gidansa, Wike inda ya ce Rivers na bukatar zaman lafiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Rivers - Gwamna Siminalayi Fubara na Rivers ya yi magana kan abubuwan da ke faruwa a jihar.

Fubara ya bukaci tsohon gwamnan Rivers, Nyesom Wike da ya hakura da maganar sai ya mallaki ikon jihar.

Kara karanta wannan

'Mene dalilin kiran sunana kadai ', Gwamna ya kalubalanci Tinubu kan rigimar Ribas

Gwamna ya shawarci mai gidansa kan rikicin jihar Rivers
Gwamna Siminalayi Fubara ya bukaci Nyesom Wike ya manta da rikicin jihar Rivers. Nyesom Wike, Sir Siminalayi Fubara.
Asali: Facebook

Gwamna Fubara ya shawarci Wike kan rikicin Rivers

Gwamnan ya bayyana haka yayin hira ta musamman da Channels TV a jiya Litinin 7 ga watan Oktoban 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Fubara ya ce ya kamata tsohon gwamna Wike ya sani ba kowane fada ba ne sai ya yi nasara a kai.

Ya ce kamata ya yi Wike ya janye daga shiga rigimar saboda kaunar da yake yi wa jihar domin samun zaman lafiya.

Gwamnan Rivers ya bukaci neman zaman lafiya

"Ina fadawa Wike akwai abin da bai kamata ana yi ba, ya kamata a wuce wannan wuri."
"Muna bukatar zaman lafiya a jihar nan, ya kamata ya sani ba kowane fada ba ne sai ka yi nasara."
"Saboda kaunar da ya ke yi wa Rivers ya kamata a bar wannan abin, bai kamata mu tarwatsa jihar ba, Fubara zai iya tafiya gobe, ba mu san waye zai zo ba."

Kara karanta wannan

'Ba ni kadai ba ne', Sheikh Gumi ya fadi wadanda ke raka shi wurin yan bindiga

- Siminalayi Fubara

Jam'iyyar AA ta lashe kujera a Rivers

Kun ji cewa hukumar zaben jihar Rivers, RSIEC ta sake sanar da zaben karamar hukuma daya da ta rage bayan kammala zabe.

Hukumar RSIEC ta sanar da cewa jam'iyyar AA ce ta yi nasara a karamar hukumar Etche bayan APP ta lashe kananan hukumomi 22.

Shugaban hukumar a jihar Rivers, Adolphus Enebeli ya ce Uzodinma Nwafor na jam'iyyar AA shi ya yi nasara a zaben da aka yi a ranar Asabar 5 ga watan Oktoban 2024.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.