Akpabio Ya Taya APC Lashe Kujera 1, PDP Ta Cinye Kujerun Ƙananan Hukumomi 30

Akpabio Ya Taya APC Lashe Kujera 1, PDP Ta Cinye Kujerun Ƙananan Hukumomi 30

  • Jam'iyyar PDP ta yi nasara yayin da aka sanar da sakamakon zaben kananan hukumomin jihar Akwa Ibom
  • Jam'iyyar ta samu nasarar lashe kujeru 30 cikin 31 na ƙananan hukumomin jihar da aka yi a jiya Asabar
  • Hukumar zaben jihar, AKISIEC ita ta sanar da sakamakon zaben a yau Lahadi 6 ga watan Oktoban 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Akwa Ibom- Hukumar zaben jihar Rivers (AKISIEC) ta sanar da sakamakon zaben kananan hukumomi.

Hukumar AKISIEC ta tabbatar da cewa jam'iyyar PDP ce ta yi nasarar lashe zaben a kananan hukumomi 30 cikin 31.

An sanar da sakamakon zaben kananan hukumomi, APC ta lashe kujera 1 yayin da PDP ta cinye 30
Jam'iyyar PDP ta lashe zaben kananan hukumomi 30 yayin da APC ta yi nasara a 1. Hoto: Pastor Umo Eno, Godswill Obot Akpabio.
Asali: Facebook

Akwa Ibom: PDP ta lashe zaben kananan hukumomi

Shugaban hukumar, Aniedi Ikoiwak shi ya tabbatar da haka a yau Lahadi 6 ga watan Oktoban 2024, cewar rahoton The Nation.

Kara karanta wannan

Gwamna ya rasa karamar hukuma a hannun bakuwar jam'iyya, APC ta karbi kujera 1

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ikoiwak ya ce jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta yi nasarar lashe karamar hukuma guda daya.

Karamar hukumar Essien Udim ita ce APC ta yi nasara inda nan ne shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya fito.

APC ta kalubalanci zaben da zargin magudi

Tun kafin gudanar da zaben, masu fashin baki a harkokin siyasa sun yi hasashen dama jam'iyyar APC za ta iya yin nasara, Punch ta ruwaito.

Har ila yau, jam'iyyar PDP mai mulkin jihar ta lashe kusan duka zaɓen kujerun kansiloli da aka gudanar a jiya Asabar.

Sai dai jam'iyyar APC ta kalubanci zaben inda zargi tafka magudi zaɓen kananan hukumomin da PDP mai mulkin jihar ta yi a jiya Asabar 6 ga watan Oktoban 2024.

An sanar da sakamakon zaben kananan hukumomi

Kun ji cewa yayin da aka sanar da sakamakon zaben kananan hukumomin jihar Rivers, jam'iyyar AA ta samu nasarar lashe kujera daya a cikin 23.

Kara karanta wannan

Benue: Jam'iyyar APC ta ba da mamaki a zaben kananan hukumomi

Hukumar zaben jihar ta RSIEC ta tabbatar da nasarar jam'iyyar AA a yau Lahadi 6 ga watan Oktoban 2024 kwana ɗaya bayan gudanar da zaben.

A jiya Asabar da aka gudanar da zaben, jam'iyyar APP ta yi nasarar lashe kujerun kananan hukumomi 22 cikin 23 da goyon bayan Gwamna Siminalayi Fubara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.