'Kwanan APC Ya Kare', Tsohon Gwamna a Arewa Ya Ce Za Su Dawo da Mulkin PDP
- Siyasar jihar Benue tana cigaba da daukar hankali musamman yayin da PDP ke sake shiri domin ganin ta kwace mulki
- Tsohon gwamnan jihar, Samuel Ortom ya bayyana himmatuwar jam'iyyarsa ta PDP na raba APC da mulki a zaben 2027
- Ortom ya roki yan jam'iyyar PDP a jihar da su kawar da duk wani bambance-bambance domin tumbuke APC a mulki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Benue - Tsohon gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom ya sha alwashin kwace mulki daga APC a zaben 2027.
Ortom ya ce alamu sun nuna yan jam'iyyar PDP sun shirya kawo karshen mulkin rashin adalci na jam'iyyar APC.
Tsohon gwamna ya sha alwashi kan zabe
Tsohon gwamnan ya bayyana haka ne yayin babban taron jam'iyyar da aka gudanar a birnin Makurdi, cewar rahoton The Guardian.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ortom ya bukaci yan jam'iyyar da su hada kai domin ganin an samu biyan bukata kan zaɓen 2027 da suka sanyawa ido.
Shugaban PDP ya na hangen 2027
Shugaban riko na jam'iyyar a jihar, Napoleon Bali ya ce jam'iyyar tana cigaba da ginuwa domin zaben 2027 da ake tunkara.
Bali ya bukaci yan jam'iyyar da US kasance tsintsiya madaurinki daya domin ganin an cimma duk abin da ake bukata musamman game da zaben 2027.
Yan siyasa sun yabawa al'umma a taron PDP
A martaninsa, Mr. David Amo a madadin al'ummar yankin Benue ta Arewa maso Gabas ya ce an gudanar da babban taron cikin tsari.
Amo ya ce yadda al'umma suka cika yayin babban taron ya tabbatar da cewa har yanzu da ranta a jihar Benue ba kamar yadda ake tsammani ba
Gwamna ya kulle kamfanonin Ortom
Kun ji cewa gwamnatin jihar Benue ta kulle kamfanin tsohon gwamna, Samuel Ortom kam zargin kin biyan haraji na makudan kudi.
Ana zargin kamfanin mai suna Oracle Business mallakin tsohon gwamna, Ortom da kin biyan haraji har N93.5m.
Sai dai wasu na ganin hakan bita da kullin siyasa ne da ake yi domin kassara harkokin kasuwancin Ortom a jihar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng