‘Mun Yi Maguɗin Zaɓe a Baya’ Tsohon Shugaban Jam’iyyar APC Ya Tona Asiri
- Tsohon shugaban jam'iyyar APC a jihar Rivers, Tony Okocha ya bayyana yadda suka hadu suka tafka maguɗin zaɓe a jihar
- Cif Tony Okocha ya yi zargin cewa sun hadu da dama yayin maguɗin zaɓen kuma har da shugaban APC na jihar da yake mulki
- Bayan tabbatar da ya yi maguɗin zaɓe, Okocha ya bayyana abin da ya kamata doka ta masa saboda karfin halin tona asirin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Rivers - Tsohon shugaban APC a Rivers ya fasa kwai yayin da ya ce jam'iyyar ta tafka maguɗin zaɓe a baya.
Tony Okocha ya ce ba zai boye abin da ya san sun aikata ba kuma kamata ya yi a yaba masa a kan hakan.
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa Tony Okocha ya yi zargin cewa shugaban APC na jihar a halin yanzu, Emeka Beke na cikin wandada suka yi maguɗin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
APC ta yi maguɗin zaɓe inji Tony Okocha
Tsohon shugaban APC na jihar Rivers ya tabbatar da cewa sun hada baki sun yi maguɗin zaɓe a jihar.
Tony Okocha ya bayyana cewa ya fadi haka ne a bayyane domin ya ja hankalin yan siyasa su guji tafka maguɗin zaɓe.
Okocha ya tabbatar da cewa lamarin ya faru ne yayin wani zaben kananan hukumomi da ya gudana a jihar.
Maguɗin zaɓe: Za a kama shugaban APC?
The Cable ta wallafa cewa Tony Okocha ya ce ya kamata a karrama shi ne bisa kokarin da ya yi na tona asirin maimakon a ce za a kama shi.
Tsohon shugaban ya buga misali da cewa kamar yadda ba za a kama barawo da ya bayyana tubansa ba, haka bai kamata a kama shi ba.
Shugaban APC na yanzu ya yi maguɗin zaɓe?
Bayan tabbatar da lamarin, Tony Okocha ya ce shugaban APC na yanzu a jihar Rivers ma tare da shi aka yi maguɗin zaɓen.
Sai dai a nan take shugaban APC a halin yanzu, Emeka Beke ya ƙaryata cewa an yi maguɗin da shi domin nasarar wata jam'yya.
Jonathan ya yi magana kan murde zabe
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon shugaban kasa, Goodluck Ebele Jonathan ya yi magana kan zaben gwamna da ya gabata a jihar Edo.
Shugaba Goodluck Jonathan ya bayyana cewa amfani da kimiyya da fasaha kawai ba za ta magance matsalolin maguɗin a zabe ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng