2027: Kwankwaso Ya Magantu kan Zama Mataimakin Obi, Ya Fadi Sharudan da Za a bi
- Jagoran siyasar jihar Kano, Rabiu Kwankwaso ya magantu kan amincewa da tayin zama mataimakin Peter Obi
- Kwankwaso ya fayyace ratan da ke tsakaninsa da Obi ta ɓangaren ilimi da kuma siyasa inda ya ce ya girme shi
- Sai dai Kwankwaso ya ce a shirye ya ke domin yin magana da kowa kan lamarin amma bisa sharuda na gaskiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Sanata Rabiu Kwankwaso ya yi magana kan zama mataimakin dan takarar shugaban kasa a LP, Peter Obi.
Rabiu Kwankwaso ya ce ba shi da matsala da hakan amma shi ba sa'ansa ba ne a siyasa har ma da bangaren ilimin boko.
2027: Kwankwaso ya fadi ratansa da Obi
Jigon jam'iyyar NNPP ya bayyana haka ne a cikin wani bidiyo da @jrnaib2 ya wallafa a shafin X a yau Juma'a 4 ga watan Satumbar 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwankwaso ya kawo misalai da suka shafi kokarin da ya yi a Kano da mukaman da ya rike inda ya kwatanta da na Peter Obi.
'Dan siyasar ya ce shi yayan Obi ne siyasa kowa ya sani har ma da ilimi amma ya ce a shirye suke su yi magana da kowa.
"Ko da ake cewa na yi wa Peter Obi mataimaki, ma ce ni ba ni da matsala amma a kawo ka'idoji, mu ne yan Arewa aka raina cewa ba mu da ilimi, amma ni yayansa ne a siyasa, a ilimi ma PhD ne da ni."
"Ba mukamai daya muka rike ba, kokarinmu ma a mulki ba iri daya ba ne kowa ya sani a jiharsa da tawa."
"Saboda haka muna jira mu yi magana da kowa amma duk abin da za a yi, a yi shi cikin gaskiya."
- Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso
Martanin yan Obidients ga maganar Kwankwaso
Wasu daga cikin magoya bayan Obi sun yi fatali da maganar Kwankwaso inda suka ce ba su bukatarsa.
@MasterMaliq:
"Ba mu bukatarka, mun gode sosai."
@IamEkene:
"Har yanzu bai fahimci abin da ya faru da shi a 2023 ba, Obi ba sa'ansa ba ne a siyasa, kamata ya yi yana hada kansa da Datti, amma lokaci zai mayar da shi mai kan-kan da kai."
@Emegzyofficial:
"Kana ganin ka fi Peter Obi amma kana tashi da kuri'u miliyan biyu yayin da Obi ya samu miliyan shida, waye babba a cikinku."
@EzeigboChigozie:
"Kwankwaso ba abin yarda ba ne a bar shi kawai, yana taya Tinubu yaki ne, a karshe zai yaudari Peter Obi."
Kwankwaso ya koka kan yadda APC ke mulki
Kun ji cewa jagora a NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya caccaki tsarin yadda jam'iyyar APC ke mulkin Najeriya a yanzu.
Kwankwaso ya koka kan yadda ake fama da tsadar rayuwa da kuma matsanancin rashin tsaro saboda sakaci na Bola Tinubu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng