An Rikita Ribas, Masu Zanga Zanga Sun Fusata, Sun Dunguma Ofishin Hukumar Zabe
- Wasu mazauna jihar Ribas sun bijirewa ruwan sama wajen nuna adawa da kokarin hana zaben ranar Asabar
- Wata kotun tarayya ta dakatar da yunkurin gwamnati Siminalayi Fubara na gudanar da zaben kananan hukumomi
- Amma gwamnan ya ce ba zai yiwu ba, za a yi zabe kamar yadda aka tsara zai gudana a ranar Asabar 5 Oktoba, 2024
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Rivers - Mazauna jihar Ribas sun shiga zanga-zanga kan yunkurin hana gudanar da zaben kananan hukumomi a jihar wanda ke cike da dambarwar siyasa.
Siyasar jihar Ribas ta dauki dumi bayan gwamnatin jihar ki bin umarnin kotu, ta kuma ce za ta gudanar da zaben kananan hukumomi a ranar Asabar 5 Oktoba, 2024.
Channels TV ta wallafa cewa gwamnan jihar, Siminalayi Fubara ya dira a ofishin hukumar zabe ta jihar da yanar daren Juma'a, inda gwamnan ya ce ya hana yan sanda kwashe kayan zabe.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ana zanga zanga a Ribas kan zabe
A yau Juma'a ne fusatattun matasa su ka tunkari ofishin hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Ribas kan lallai sai an gudanar da zaben kananan hukumomi.
Duk da mamakon ruwan sama da ake yi, matasan sun shiga ciki su na rera wakokin "Dole a yi zabe" kamar yadda aka tsara za a yi a jihar.
Ana fuskantar matsala kan zabe a Ribas
Gwamna Siminalayi Fubara ya kafe kan sai an gudanar da zaben kananan hukumomi a jihar inda 'yan sanda suka ce ba za su shiga ba.
Wannan lamari ya raba kan jihar, inda wasu ke goyon bayan a gudanar da zaben a gobe Asabar, jam'iyyun siyasa kuma na cewa ba zai yiwu ba.
Masu zanga zanga sun nufi ofishin DSS
A baya mun wallafa cewa magoya bayan jam'iyyar PDP sun bayyana rashin amincewa da shirin gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara duk da kotu ta dakatar da haka.
Fusatattun yan siyasa sun gudanar da zanga-zanga zuwa ofishin rundunar yan sandan jihar da ofishin hukumar tsaron farin kaya (DSS) domin bayyana damuwarsu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng