'Tinubu bai San Me Yake Faruwa ba?' Mai Neman Takarar Shugaban Kasa Ya Dauki Zafi

'Tinubu bai San Me Yake Faruwa ba?' Mai Neman Takarar Shugaban Kasa Ya Dauki Zafi

  • Tsohon dan majalisar wakilai, Dakta Usman Bugaje ya yi zazzafan martani kan jawabin shugaban kasa na ranar 1 ga Oktoba
  • Dakta Usman Bugaje ya ce bayanin da shugaba Bola Tinubu ya yi a ranar yanci ya nuna kamar bai san halin da Najeriya ke ciki ba
  • Haka zalika 'dan siyasar ya yi kira ga Bola Tinubu kan yin gaggawa wajen warware matsalolin da suka addabi yan Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu na cigaba da shan suka kan bayanin da ya yi na ranar 1 ga Oktoba na shekarar bana.

Dakta Usman Bugaje wanda ya nemi tikitin takara a PRP a 2023 ya ce bayanin da shugaban kasar ya yi alama ce da ke nuna cewa bai san halin da Najeriya ke ciki ba.

Kara karanta wannan

'Ko shekaru 100 ka ba Tinubu bai san yadda zai yi da Najeriya ba'

Bugaje
Usman Bugaje ya yi raddi ga Bola Tinubu. Asiwaju Bola Ahmed Tinubu|Usman Bugaje
Asali: Facebook

Channels Television ce ta wallafa bidiyon Dakta Usman Bugaje a wata hira da suka yi kan matsalolin Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Usman Bugaje ya yi raddi ga Tinubu

Dakta Usman Bugaje ya ce kwata kwata Bola Tinubu bai dauko hanyar warware matsalolin Najeriya ba cikin bayanin da ya yi ranar 1 ga Oktoba.

Masanin tarihin ya ce maimakon Bola Tinubu ya rika fadin yadda zai magance matsalolin kasa sai ya koma yana lissafa su.

Tinubu ya san me yake faruwa a Najeriya?

Hon. Usman Bugaje ya ce kwata kwata maganar da Bola Tinubu ya yi bai nuna alamar ya san me ke faruwa a Najeriya ba.

Bugaje ya ce maimakon Tinubu ya mayar da hankali kan tsadar rayuwa, ambaliya da ta faru a Maiduguri da jihohi sai ya rika ambatan abubuwa marasa muhimmanci.

Kara karanta wannan

Na kusa da Tinubu ya fadi lokacin da za a yi garambawul a majalisar Ministoci

Magana kan sayen jirgin Bola Tinubu

Sannan Bugaje ya ce sayen jirgi da Tinubu ya yi ana wahala a Najeriya ma alama ce da ke nuna bai san halin da ake ciki ba.

Ya ce idan ya san halin yunwa da ake ciki da wahalar rayuwa ba zai saye jirgi ba a yayin da mutane ke gaza samun abinci.

Tinubu ya sauke harajin VAT a wasu abubuwa

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta fitar da sanarwar cire harajin VAT a wasu kayayyaki domin kawo saukin rayuwa ga talakawa.

Daraktan yada labaran ma'aikatar kudi ta kasa ne ya fitar da sanarwar tare da cewa hakan na cikin kokarin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng