Kwankwaso Ya Bayyana Abin da 'Yan Najeriya Za Su Yiwa APC a 2027
- 'Dan takara a 2023, Jagoran jam'iyyar NNPP na ƙasa, Rabiu Musa Kwankwaso, ya caccaki APC mai mulki a Najeriya
- Kwankwaso ya bayyana cewa APC ta wahalar da ƴan Najeriya kuma za su sauya ta a zaɓen shekarar 2027 da ke tafe
- Ya bayyana cewa a bayyana yake APC ba ta son talakawa kuma ƴan Najeriya za su yi fafutukar ganin sun kawar da ita
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NNPP a zaɓen 2023, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya yi magana kan halin ƙuncin da ake ciki a ƙasar nan.
Kwankwaso ya bayyana cewa duba da halin da ake ciki a ƙasar nan, ƴan Najeriya za su yunƙuro domin kawo sauyi a 2027.
Kwankwaso ya bayyana haka ne a lokacin da yake karɓar dimbin ƴaƴan jam’iyyar APC da suka sauya sheƙa zuwa jam’iyyar NNPP a jihar, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rabiu Kwankwaso ya caccaki APC
'Dan siyasar ya tarbi ƴan jam’iyyar APC da suka sauya sheƙar ne daga ƙananan hukumomin Dala, Kiru da Gwale a gidansa da ke Miller Road a Kano.
"Yan Najeriya musamman ƴan Arewa sun sha wahala sosai kuma babu wani matsin lamba ko tsoratarwa da zai sa su canja ra’ayinsu."
"Ya kamata ƴan Najeriya su sake tunani kan yadda abubuwa suke a halin yanzu, yanzu ta bayyana a fili cewa gwamnatin APC ba ta son talakawa kuma ba za ta taɓa canzawa ba."
"Yanzu ta tabbata cewa duk da shirinsu na amfani da jami’an tsaro da INEC a zaɓe mai zuwa, hakan ba zai yiwu ba saboda ƴan Najeriya sun gaji kuma tabbas za su yi fafutukar kawo sauyi."
- Rabiu Musa Kwankwaso
Kwankwaso ya hango nasara a 2027
A wani labarin kuma, kun ji cewa jagoran jam'iyyar NNPP, Rabi'u Kwankwaso, ya yi magana kan babban zaben Najeriya na 2027 da ke tafe.
Tsohon gwamnan jihar na Kano ya bayyana cewa jam'iyyar NNPP za ta taka rawar gani a zaben 2027 domin ta dauki manyan matakai.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng