PDP da APC Sun Hada Kai domin Kalubalantar Matakin Gwamna kan Zabe
- Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers na fuskantar matsala daga jam'iyyun PDP da kuma APC kan zaben ƙananan hukumomi
- Jam'iyyun guda biyu sun kalubalanci gwamnan kan shirin gudanar da zaben a ranar 5 ga watan Oktoban 2024 duk da hukuncin kotu
- Hakan ya biyo bayan fatali da umarnin kotu da gwamnan ya yi kan cigaba da shirin gudanar da zaben a ranar Asabar mai zuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Rivers - Yayin da ake shirin gudanar da zabukan kananan hukumomi a jihar Rivers, APC da PDP sun hade baki.
Jam'iyyar APC mai adawa da PDP mai mulkin jihar sun kalubalanci shirin gudanar da zaben kananan hukumomin Ribas.

Asali: Facebook
PDP da APC sun hada kai a Rivers
The Guardian ta ruwaito cewa jam'iyyun biyu na kalubalantar Gwama Siminalayi Fubara kan dogewa cewa sai an yi zabukan da aka shirya yi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakan ya biyo bayan shirin gudanar da zaben a ranar Asabar 5 ga watan Oktoban 2024 duk da umarnin kotu a cewar rahoton Punch.
Shugaban riko na jam'iyyar APC a jihar, Cif Tony Okocha ya kalubalanci Fubara duba da hukuncin kotu kan dakatar da zaben da aka yi niyya.
A bangarensa, shugaban PDP a jihar, Chukwuemeka Aaron ya ce akwai kura-kurai a shirin gudanar da zaben inda ya ce jam'iyyarsu ba za ta shiga ba.
Gwamna Fubara ya sha alwashi kan zaben
Duk da barazanar jam'iyyun guda biyu, a jiya Laraba 2 ga watan Oktoban 2024 Gwamna Fubara ya ba da tabbacin gudanar da zaben
Wannan umarni na gwamnan ya fara sanya fargaba a zukatan yan jihar saboda tsoron tashe-tashen hankula.
Gwamna Fubara ya ba da hukun zabe
Kun ji cewa Gwamnan jihar Ribas ya ayyana Alhamis da Jumu'a a matsayin ranakun hutu domin ba ma'aikata damar komawa yankunansu.
Siminalayi Fubara ya ce ya ɗauki wannan matakin ne domin mutane su koma gida su kaɗa kuri'unsu a zaɓen kananan hukumomi.
Ya kuma sanar da taƙaita zirga-zirgar ababen hawa daga tsakar daren ranar Juma'a zuwa ƙarfe 5:00 na yammacin ranar Asabar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng