Jam'iyyar PDP Ta Yi Nasara kan APC Ana Shirin Zaben Gwamna
- Jam'iyyar PDP a jihar Ondo ta yi murnar karɓar mambobin jam'iyyar APC sama da 200 waɗanda suka raba gari da ita
- Masu sauya sheƙar dai sun yi hujja da rigingimun cikin gida da suka dabaibaye jam’iyyar APC wajen canza gidan
- Ana kallon wannan guguwar sauya sheƙar a matsayin babban ci gaba ga PDP gabanin zaɓen gwamna a Ondo
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Ondo - A wani babban ci gaban siyasa, jam’iyyar PDP a jihar Ondo ta karɓi masu sauya sheƙa daga APC a ranar Litinin, 30 ga watan Satumban 2024.
Jam’iyyar PDP ta yi maraba da tsohon shugaban hukumar raya yankin Neja-Delta (NDDC), Dakta Benson Enikuomehin, tare da magoya bayansa sama da 200 zuwa cikin ta.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da jam'iyyar PDP ta fitar a shafinta na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa suka fice daga APC zuwa PDP?
Masu sauya sheƙar waɗanda a baya ƴaƴan jam’iyyar APC ne, sun bayyana dalilai daban-daban da suka sanya suka komawa PDP mai adawa a jihar.
Sun bayyana cewa sun yanke shawarar ne saboda rigingimun cikin gida da suka dabaibaye APC da kuma burin samun inda za a riƙa damawa da su.
Sauya sheƙar dai wani wani gagarumin ci gaba ne ga jam’iyyar PDP a ƙoƙarin da take yi na samun nasara a zaɓen gwamnan jihar da ke tafe.
Dakta Benson Enikuomehin, wanda fitaccen 'dan jam'iyyar APC ne kuma tsohon shugaban hukumar NDDC, shi ne ya jagoranci masu sauya sheƙar zuwa PDP.
Ciyamomi sun fice daga jam'iyyar PDP
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu daga cikin shugabannin ƙananan hukumomi na riƙon ƙwarya waɗanda Gwamna Siminalayi Fubara ya naɗa a jihar Ribas sun fice daga PDP.
Rahotanni sun nuna kantomomin sun sauya sheka daga PDP zuwa jam'iyyar APP a lokacin da ake shirye-shiryen zaben kananan hukumomi ranar 5 ga watan Oktoba, 2024.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng