‘Yan Damfara ne,’: NNPP a Kano Ta Gargadi Barau kan Karbar Masu Canza Sheka

‘Yan Damfara ne,’: NNPP a Kano Ta Gargadi Barau kan Karbar Masu Canza Sheka

  • Jam'iyyar NNPP a jihar Kano ta yi magana kan mutanen da suke sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya
  • Shugaban jam'iyyar NNPP a Kano, Hashimu Dungurawa ya ce ƴaƴan NNPP suna hade waje guda a dukkan sassan jihar Kano
  • Dungurawa ya yi jawabi ne yayin da yake karɓar wasu yan jam'iyyar APC zuwa NNPP a karamar hukumar Dawakin-Tofa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Jami'yyar NNPP ta yi zazzafan martani kan cewa ƴaƴanta suna sauya sheka zuwa APC.

Shugaban NNPP, Hashimu Dungurawa ya ce sam ba gaskiya cikin lamarin domin kansu a hade yake a jihar Kano.

Kara karanta wannan

Abba ya yiwa Ganduje illa a siyasa, tulin 'yan APC sun sauya sheka a mahaifarsa

Barau Jibrin
NNPP ta gargadi Sanata Barau kan sauya sheka. Hoto: Barau I.Jibrin
Asali: Twitter

Legit ta samo martanin da NNPP ta yi ne a cikin wani sako da daraktan yada labaran Kano, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya wallafa a Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NNPP ta ce ƴaƴanta ba su sauya sheka

Jami'yyar NNPP a jihar Kano ta fitar da matsaya kan ƴaƴanta da ake cewa suna sauya sheka a Abuja zuwa APC.

Shugaban NNPP, Hashimu Dungurawa ya ce sam ba gaskiya cikin labarin domin har yanzu ba su ga ko mutum daya ya ragu a cikinsu ba.

Ga abin da yake cewa:

Mun ji labari wani mutum a Abuja (Sanata Barau Jibrin) yana karbar yan NNPP zuwa APC amma wannan labarin ba gaskiya ba ne.
Mun duba rajistar mambobinmu amma har yanzu ba muga ko daya ya ragu ba.

- Hashimu Dungurawa, Shugaban NNPP a Kano.

Kara karanta wannan

Rikicin NNPP: Yan majalisa 2 sun fice daga jam'iyyarsu Kwankwaso, sun koma APC

NNPP ta ba Sanata Barau Jibrin shawara

Shugaban NNPP, Hashimu Dungurawa ya ce ya kamata idon Sanata Barau Jibrin ya bude a kan mutanen da yake karba a Abuja.

Dungurawa ya ce kyau Sanata Barau ya yi hankali da yan damfara masu zuwa suna karbar kudi a wajensa da sunan sauya sheka.

'Yan APC sun koma NNPP a Kano

A wani rahoton, kun ji cewa NNPP mai mulki a jihar Kano ta kara samun ƙarfi yayin da ta karbi dubban mutane daga jam'iyyar adawa ta APC.

An ruwaito cewa mutanen da suka sauya sheƙar sun hada da manyan yan siyasa da suka rike mukamai mabanbanta a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng