Abba Ya yiwa Ganduje Illa a Siyasa, Tulin ’Yan APC Sun Sauya Sheka a Mahaifarsa
- Jami'yyar NNPP mai mulki a jihar Kano ta kara samun ƙarfi yayin da ta karbi dubban mutane daga jam'iyyar adawa ta APC
- An ruwaito cewa mutanen da suka sauya sheƙar sun hada da manyan yan siyasa da suka rike mukamai mabanbanta a jihar
- NNPP ta nuna farin ciki da karbar mutanen kasancewar sun fito ne daga yankin shugaban APC na kasa, Abdullahi Ganduje
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Ana cigaba da samun masu sauya sheka a Kano yayin da ake tunkarar zaben kananan hukumomin jihar.
Wasu 'ya'yan jam'iyyar APC mai adawa a jihar sun koma NNPP bisa dalilin cewa shugaban APC bai kyautata musu ba.
Legit ta gano lamarin ne a cikin wani sako da daraktan yada labaran gwamnatin Kano, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya wallafa a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan APC sun koma NNPP a Kano
Jam'iyyar NNPP mai mulki a jihar Kano ta karbi 'yan APC mutum 1,331 duka sauya sheka saboda dalilan siyasa.
An ruwaito cewa mutanen da suka sauya shekar sun fito ne daga karamar hukumar shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje.
Bayan shiga NNPP, yan siyasar sun yi alkawarin yakar jam'iyyar APC a zaɓen 2027 ta inda za su tabbatar NNPP ta kara samun nasara karo na biyu.
Dalilin sauya shekar 'yan APC a Kano
Cikin mutane da suka sauya shekar sun hada da tsohon mataimakin shugaban karamar hukumar Dawakin-Tofa da wasu jiga jigan yan siyasa.
Yan siyasar sun bayyana cewa sun fice daga APC ne saboda halin ko-in-kula da Ganduje ya nuna ga karamar hukumar Dawakin-Tofa a shekaru takwas da ya yi.
Haka zalika sun kara da cewa Abdullahi Ganduje ya gaza magance matsalolin da suka addabi jam'iyyar a cikin gida kullum sai karuwa suke yi,
APC ta shirya domin zaben Kano
A wani rahoton, kun ji cewa jami'yyar APC mai adawa ta fadi irin shirye shiryen da ta ke domin tunkarar zaben kananan hukumomi a jihar Kano.
Shugaban APC a Kano. Abdullahi Abbas ya ce sun shirya tsaf domin ka da kuri'a da kuma tabbatar da ba a sace musu kuri'a ko a yi maguɗi ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng