Jerin Zabukan da Za a Gudanar Kafin 2027 da Ake Hasashen APC Za Ta Iya Yin Nasara
An gudanar da zaben jihar Edo a ranar 21 ga watan Satumbar 2024 inda jam'iyyar APC ta yi nasara.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Hukumar INEC ta sanar da Monday Okpebholo a matsayin wanda ya lashe zaben inda dan takarar PDP, Asue Ighodalo ke biye masa.
Kafin zaben 2027, za a gudanar da zaben gwamnonin jihohi akalla hudu wanda ake ganin APC za ta iya samun nasara.
Legit Hausa ta binciko muku jihohin da za a yi zaben gwamna kafin 2027.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
1. Ondo - 2024
A ranar 16 ga watan Nuwambar 2024 ake sa ran gudanar da zaben gwamnan jihar Ondo.
Gwamna Lucky Aiyedatiwa na APC zai sake tsayawa takara a zaɓen inda tsohon mataimakin gwamna, Agboola Ajayi ke takara a PDP.
2. Anambra - 2025
Jam'iyyar APC ta sha alwashin lashe zaben gwamnan jihar Anambra kamar yadda shugabanta, Abdullahi Ganduje ya fada.
Gwamna Charles Soludo na jam'iyyar APGA yana neman sake tsayawa takara karo na biyu a jihar.
3. Ekiti - 2026
A tsakiyar shekarar 2026 ake sa ran za a gudanar da zaben gwamnan jihar Ekiti da ke Kudu maso Yammacin Najeriya.
Gwamna Biodun Oyebanji na jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya yana neman takara karo na biyu a zabe da za a gudanar a jihar.
4. Osun - 2026
Gwamna Ademola Adeleke na jam'iyyar PDP zai sake neman takara a zaɓen jihar Osun bayan yin nasara kan tsohon gwamna a APC, Gboyega Oyetola.
Duk da jam'iyyar PDP ke mulkin jihar amma ba a cire tsammanin APC ta taka rawar gani a zaben ba, watakil Oyetola ya nemi dawowa karagar mulki.
Jam'iyyar LP ta zargi Obi kan faduwa zaɓe
Kun ji cewa tsagin jam'iyyar LP ta zargi dan takarar shugaban kasa, Peter Obi da ba da gudunmawa wurin faduwarta a zaben Edo.
Jam'iyyar ta kuma zargi dan takarar gwamna a LP, Olumide Akpata kan rashin taka rawar gani a zaben da aka gudanar.
Shugaban tsagin jam'iyyar, Julius Abure ya ce faduwar LP a zaben ba ta rasa nasaba da son mulki da cin amana da Obi ke yi mata.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng