Kai Tsaye: Yadda Zaben Gwamna Ke Gudana Yau a Edo, PDP da APC Sun Ja Daga
Edo - Rana ba ta ƙarya, a yau Asabar, 21 ga watan Satumba, 2024 al'ummar Edo za su nufi rumfunan zaɓe domin yanke wanda zai jagorance su na shekaru hudu masu zuwa.
Ana ganin zaɓen gwamnan Edo a wannan karon zai yi zafi matuƙa musamman a tsakanin manyan ƴan takara uku na PDP, APC da kuma Labour Party.
Manyan ƴan takara da fafatawar za ta fi zafi a tsakaninsu sun haɗa da;
1. Asue Ighodalo - PDP
2. Sanata Monday Okpebholo - APC
3. Olumide Akpata - LP
Yayin da PDP da Gwamna Obaseki ke kokarin ci gaba da mulki, jam'iyyar APC na faɗi tashin ƙwato jihar Edo wanda ta subuce mata a 2020.
Tuni dai marubutan Legit Hausa Hausa suka shirya tsaf domin kawo muku abubuwan da ke wakana tun daga shirye-shirye, fitowar jama'a da sakamako.
Gwamna Obaseki ya kaɗa kuri'a
Gwamnan jihar Edo mai barin gado, Godwin Obaseki ya kaɗa kuri'a a zaɓen gwamnan da ke gudana yanzu yanzu a jihar yau Asabar.
Obaseki ya kada kuri’arsa ne da misalin karfe 11:57 na safe a rumfar zabe ta 19, Ward 4, Oredo, da ke cikin makarantar firamare ta Emokpae a birnin Benin City.
Obaseki ya ce ya gamsu da yadda ake gudanar da zaben, yana mai bayyana fatan ba za a samu matsala ba a lokacin tattara sakamako, Punch ta ruwaito.
Na'urar BIVAS ta ƙi yin aiki
An bar masu kaɗa ƙuri'a cikin takaici a mazaɓa ta 7, a rumfar zaɓe ta 39, saboda na'urar BIVAS ta gaza yin aiki.
Jaridar The Punch ta ce mutane 839 da suka yi rajista domin kaɗa ƙuri'a sun zazzauna a kewayen wajen yayin da suke jiran wata na'urar daga INEC.
Jami’in hukumar zaɓen da ke rumfar zaɓen ya tabbatar da cewa za a kawo sabuwar na’ura domin gudanar da zaɓen, tare da bayyana fatan za a tsawaita lokacin kaɗa ƙuri’a
Oshiomhole ya yaba yadda zabe ke tafiya a Edo
Tsohon gwamnan Edo kuma jagoran APC a jihar, Sanata Adams Oshiomhole ya ce ya gamsu da yadda harkokin zaɓe ke tafiya bayan ya kaɗa kuri'arsa.
Oshiomhole, Sanata mai wakiltar Edo ta Arewa ya ce yana fatan zaben ya tafi a haka har a kammala shi cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Ɗan takarar LP ya kaɗa ƙuri'a
Ɗan takarar gwamna na jam'iyyar Labour Party (LP), Olumide Akpata ya kaɗa ƙuri'arsa.
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa Olumide Akpata ya kaɗa ƙuri'arsa ne a rumfar zaɓensa da ke mazaɓa ta 06 a ƙaramar hukumar Oredo ta jihar.
Jami'an EFCC sun cafke masu siyan ƙuri'u
Jami'an hukumar EFCC sun cafke wasu da ake zargin masu siyan ƙuri'u ne a zaɓen gwamnan jihar Edo.
Jami'an na EFCC sun cafke mutanen ne a ƙaramar hukumar Egor ta jihar da misalin ƙarfe 10:00 na safe.
Jami'an sun tafi da mutane uku da suka haɗa da maza biyu da mace. Mutanen wajen dai sun yi turjiya kafin a cafke waɗanda ake zargin.
Dan takarar APC ya kaɗa kuri'a
Sanata Monday Okpebholo, ɗan takarar gwamna a inuwar APC a zaben Edo ya kaɗa kuri'arsa a rumfar zaɓe ta 1, gunduma ta 1 a ƙaramar hukumar Esan ta Arewa.
Ɗan takarar dai ya biya layi sannan ya jefa kuri'arsa a zaben gwamnan wanda ya kankama a mafi asakarin yankunan jihar Edo yau Asabar, in ji Channels tv.
Kayan zabe ba su iso da wuri ba
Bayanan daga Punch sun ce ruwan sama ya kawo jinkiron aiko da kayan zabe a wasu mazabu da ke yankin Edo ta tsakiya a yau.
A mazabar akwai kananan hukumomin Esan South-East, Igueben and Esan North-East, Esan West da Esan Central.
'A yi zabe a wuce gida'
‘Yan sanda sun umarci jama’a su wuce gida da zarar sun kada kuri’arsu a zaben sabon gwamnan da ake yi, Daily Trust ta kawo rahoton
DIG Frank Mba ya bayyana wannan a lokacin da aka zanta da shi game da zaben.
Yan sanda sun kama ƴan daba da makamai
Dakarun ƴan sanda sun yi ram da wasu miyagin ƴan daba biyu jiya da daddare a kokarinsu na tabbatar da an yi zaɓe lami lafiya.
Ƴan daban da suka shiga hannu, Edwin Obanor, ɗan shekara 43 da Audu Tajudeen, ƴaƴan PDP ne da suka fito daga Ugbogbo a yankin Igara Akoko
A sanarwar da aka wallafa a shafin rundunar na X, ƴan sandan sun kwato mugayen makamai daga hannun tsagerun da suka haɗa da da bindigu kirar cikin gida da alburusai.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da aka gama shirin kaɗa kuri'a domin tantance wanda zai ja ragamar jihar Edo na tsawon shekaru huɗu masu zuwa.
Babu jami'an INEC a rumfar zaɓen ɗan takarar PDP
A yanzu haka babu jami'an hukumar INEC a rumfar zaɓen ɗan takarar gwamna na jam'iyyar PDP, Asue Ighodalo, da ke ƙauyen Idinrio a Ewohimi cikin ƙaramar hukumar Esan ta Gabas a jihar Edo.
Wakilan tashar Channels tv ya ce babu alamun jami'an INEC da sauran masu ruwa da tsaki na jam'iyyu a wajen.
EFCC ta tura jami'ai domin hana siyan kuri'u
Hukumar yaƙi da masu yiwa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) ta tura jami'anta domin hana siyan ƙuri'u a zaɓen gwamnan jihar Edo.
Hukumar ta tura jami'an ne a dukkanin ƙananan hukumomin jihar a domin zaɓen na ranar Asabar, 21 ga watan Satumban 2024.
A wata sanarwa a shafinta na Facebook, Shugaban EFCC, Ola Olukoyade, ya ce an tura jami'an ne domin sanya ido da kuma hana ba masu kaɗa ƙuri'a kuɗi domin su zaɓi wani ɗan takara.
Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng
Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262