KAI TSAYE: Sakamakon Zaben Gwamnan Jihar Edo daga Gundumomi da Kananan Hukumomi

KAI TSAYE: Sakamakon Zaben Gwamnan Jihar Edo daga Gundumomi da Kananan Hukumomi

Benin, EdoA yau Asabar, 21 ga Satumbar 2024 za a fafata a zaben gwamnan Edo inda manyan 'yan takara ke kokarin gadar mulkin jihar daga Godwin Obaseki.

Manyan 'yan takara uku da ake ganin za su gwabza a zaben sun hada da Asue Ighodalo na PDP, Monday Okpebolo na APC da Olumide Akpata na jam’iyyar Labour (LP).

Sakamakon zaben gwamnan jihar Edo daga gundumomi da kananan hukumomi
Manyan ‘yan takara uku da ke neman kujerar gwamnan Edo sun hada da Asue Ighodalo (PDP), Monday Okpebholo (APC), da Olumide Akpata (LP). Hoto: Sen, Monday Okpebholo Edo, Asue Ighodalo, Olumide Akpata
Asali: Facebook

Ku kasance tare da Legit Hausa domin duba sakamakon zaben jihar Edo da ke shigowa daga runfuna, gundumomi da kananan hukumomi.

APC ta lashe rumfar Philip Shaibu

Rahoton da ke shigo mana yanzu na nuni da cewa jam'iyyar APC ta samu nasara a rumfar zaben mataimakin gwamnan Edo, Philip Shaibu.

Ward 11, PU05, karamar hukumar Etsako ta Yamma:

APC: 1138

ADC: 1

LP: 4

ADP: 3

APGA: 1

PDP: 24

Okpebolo ya lashe zabe a rumfar Oshiomhole

The Cable ta ruwaito cewa dan takarar APC, Monday Okpebolo ya samu nasara a rumfar zaben Adams Oshiomhole, tsohon gwamnan jihar ta Edo.

Ga sakamakon zaben rumfar 01, Ward 10, karamar hukumar Etsako ta Yama:

APC: 403

PDP: 1

ADC: 1

Dan takarar PDP ya lashe rumfar zabensa

The Cable ta ruwaito cewa dan takarar gwamnan Edo na jam'iyyar PDP, Asue Ighodalo ya samu nasarar lashe rumfar da ya ke zabe.

A rumfarsa ta PU3, Ward 1, Ewohimi, karamar hukumar Esan ta Kudu maso Gabas, sakamakon zaben ya nuna cewa:

PDP - 200

APC - 45

Rumfa ta 031, karamar hukumar Uhunmwonde

Jam'iyyar PDP ta samu nasara a rumfa ta 031, gundumar Omagbae ta Kudu, karamar hukumar Uhunmwonde.

PDP - 87

APC - 15

LP - 12

PU 024, Ward 02, karamar hukumar Egor

Sakamakon zaben rumfa ta 024, Ward 02, Evbareke, karamar hukumar Egor:

PDP - 35

APC - 27

LP - 6

Okpebholo : Dan takarar APC ya kawo rumfarsa

Dan takarar jam'iyyar APC a zaben gwamnan Edo da ke gudana, Monday Okpebholo ya samu nasarar lashe zaben rumfarsta ta 001, Uwessan 1, karamar hukumar Esan ta tsakiya.

Ga sakamakon zaben rumfar kamar yadda The Cable ta rahoto.

APC: 102

PDP: 1

LP: 1

PDP ta lashe zabe a mazabar Ward 1 da ke Ewohimi

Jam'iyyar PDP ta yi nasarar lashe zaben da aka yi a rumfar Ward 1 da ke Ewohimi a karamar hukumar Esan ta Kudu maso Gabas.

Premium Times ta ruwaito yadda sakamakon ya kasance:

PDP - 201

APC - 30

LP - 1

INEC ta fara dora sakamakon zabe

Da misalin karfe 4:12 na yamma, an shigar da jimillar kashi 50.67 (2,439 cikin 4,519) na sakamakon zaben gwamnan Edo zuwa shafin IReV na INEC.

INEC ta kawo tsarin wallafa sakamakon zabe kai tsaye domin tabbatar da cewa an gudanar da zaben ba tare da magudi ko aringizon kuri'u ba.

Masu bibiyar zaben jihar Edo na iya garzayawa shafin IReV na hukumar INEC domin duba sakamakon daga dukkanin rumfunan zaben jihar.

PDP ta zarce APC yawan kuri'u a GRA/Etete

Jam'iyyar PDP ta samu nasara a rumfar zabe mai lamba 05, gunduma ta 2, GRA/Etete da ke karamar hukumar Oredo, inji The Cable.

PDP - 58

APC - 15

LP - 12

PDP ta lashe zabe a rumfar Gwamna Obaseki

The Cable ta rahoto cewa Gwamna Godwin Obaseki ya kawowa PDP rumfarsa mai lamba 19, a gunduma ta 4, karamar hukumar Oredo.

PDP - 127

APC - 37

LP - 11

PDP ta sake lashe rumfar zabe a Etsako ta Yamma

Jam'iyyar PDP ta yi nasara a mazabar Ward 3, Unit 21 a karamar hukumar Etsako ta Yamma.

Ya yadda sakamakon ya kasance, kamar yadda TheCable ta ruwaito.

PDP - 30

APC - 28

LP - 11

PDP ta samu nasara a rumfar Idumuoka PHC

Asue Ighodalo, dan takarar jam’iyyar PDP, ya yi nasara a rumfar zabe da ke cibiyar lafiya ta Idumuoka a karamar hukumar Igueben a jihar Edo.

Sakamakon da aka bayyana a rumfar zaben, Ighodalo ya samu kuri’u 104 inda ya doke Monday Okpebholo na APC wanda ya samu kuri’u 34 yayin da Olumide Akpata na jam’iyyar Labour ya zo na uku da kuri’u hudu.

Dan takarar LP ya rasa mazabarsa

Dan takarar gwamna a jam'iyyar LP, Olumide Akpata ya rasa mazabarsa ga ɗan PDP, Asue Ighodalo.

Dan takarar gwamna a jam'iyyar LP, Olumide Akpata ya rasa mazabarsa ga ɗan PDP, Asue Ighodalo.Dan takarar gwamna a jam'iyyar LP, Olumide Akpata ya rasa mazabarsa ga ɗan PDP, Asue Ighodalo.

Ya yadda sakamakon ya kasance kamar yadda TheCable ta ruwaito:

Ya yadda sakamakon ya kasance:Ya yadda sakamakon ya kasance:

PDP - 41

APC - 19

LP - 32

PDP ta samu nasara a rumfar Egbiki HC

Sakamakon zaben rumfar Egbiki HC, gundumar Ekekhen, karamar hukumar Igueben.

PDP - 36

APC - 17

Mutane 53 ne suka kada kuri'a.

PDP ta lashe rumfar Idumuoka PHC

Sakamakon zabe daga rumfar Idumuoka PHC da ke gundumar Afuda/Idumuoka, karamar hukumar Igueben ya nuna cewa PDP ta samu kuri'u 105.

Fredrick Lugard, wanda ya wallafa samakon ya ce PDP ta samu mafi rinjayen kuri'u a rumfar zaben duk da cewa an samu masu sayen kuri'u daga 'yan adawa.

Sakamakon zaben rumfar.

PDP - 105

APC - 34

LP - 4

ADC - 2

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.