Gwamna a Arewa Zai Sauya Sheka daga PDP Zuwa APC? An Ji Gaskiyar Lamari
- Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Plateau ya musanta rade-radin cewa ya koma jam'iyyar APC daga PDP
- Mista Mutfwang ya ce kwata-kwata babu kamshin gaskiya a cikin labarin da ake yadawa a kafofin sadarwa
- Wannan na zuwa ne bayan yada wasu hotuna dauke da hoton gwamnan da ake cewa ya sauya sheka zuwa APC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Plateau - Gwamnatin jihar Plateau ta yi martani kan jita-jitar cewa Gwamna Caleb Mutfwang zai koma APC.
Gwamna Mutfwang ya musanta labarin da ake yadawa inda ya ce yana nan daram a jam'iyyarsa ta PDP mai hamayya.
Gwamnan Plateau ya musanta komawa APC
Daraktan yada labaran gwamnan, Gyang Bere shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da Channels TV ta samu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bere ya ce wannan labarin kanzon kurege ne kuma babu kamshin gaskiya a cikinsa.
"An shirya karyar ce da manakisa domin kawo rarrabuwa tsakanin Gwamna Caleb da shugabancin jam'iyyar PDP."
"Duk da wannan karairayi ba su cancanci martani ba amma ya zama dole saboda kawar da mutane daga bata."
- Cewar sanarwar
Plateau: Gwamnan ya roki al'umma kan jita-jitar
Sanarwar ta bukaci al'umma da su yi watsi da labarin inda ta ce niyyarsu shi ne bata sunan gwamna da mutuncinsa.
Ta ce Gwamna Mutfwang bai ba kowa izinin wallafa hoton ba inda ta ce Caleb yana nan daram a jam'iyyarsa ta PDP.
Hadimin gwamnan ya ce ana neman kawo baraka ne tsakanin Mutfwang da kuma jam'iyyar PDP a jihar.
Wannan na zuwa ne bayan yada wani hoton gwamnan a kafofin sadarwa da aka ce ya koma APC mai mulkin Najeriya.
Gwamna Caleb ya kori ciyamomi a Plateau
Kun ji cewa Gwamnatin jihar Plateau ta kori dukan shugabannin kananan hukumomi 17 a jihar bayan wa'adinsu ya kare.
Gwamna Caleb Mutfwang shi ya ba da wannan umarni inda ya godewa tsofaffin shugabannin kananan hukumomin.
Hakan na kunshe a cikin wata sanarwa da sakataren yada labaransa, Gyang Bere ya fitar a daren ranar Juma'a ga watan Satumbar 2024.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng