Shugaban Kasa Tinubu Ya Tsawatarwa Yan Siyasa Ana Saura a yi Awanni Zaben Edo
- Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya ja kunnen yan siyasa a jihar Edo kan gudanar da zabe cikin lumana
- Shugaban ta sanarwar da hadiminsa,Bayo Onanuga ya fitar, ya ce ba a samun yalwar arziki sai da zaman lafiya
- A ranar Asabar, 21 Satumba 2024 mazauna jihar Edo za su fita rumfunan zabe domin zabar sabon gwamna
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Edo - Shugaban kasar nan, Bola Ahmed Tinubu ya bukaci masu ruwa da tsaki sun tabbatar an yi zaben Edo bisa adalci. Shugaban ya jaddada muhimmancin zaman lafiya yayin gudanar da zaben gwamnan jihar a Edo.
A sakon da hadimin shugaban, Bayo Onanuga ya wallafa a shafinsa na X, ya bayyana cewa ana samun ci gaba ne kawai idan akwai zaman lafiya.
Bola Tinubu ya ja kunnen yan siyasar Edo
Jaridar This day ta wallafa cewa shugaban kasa, Bola Tinubu ya gargadi yan siyasa kan tayar da hankula yayin zaben Edo a gobe Asabar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya gargadi wakilan jam'iyyun siyasa da su guji tayar da tarzoma lokutan zaben, domin yan kasa su na da yancin zabar wanda zai wakilce su.
Edo: Shugaba Tinubu ya shawarci masu zabe
Shugaban kasa, Bola Tinubu ya shawarci yan jihar Edo da za su zabi wanda su ke so a matsayin gwamna da su bi doka da oda wajen kada kur'arsu.
Tinubu ya jaddada cewa ba shi da shakku kan ingancin hukumar gudanar da zabe mai zaman kanta (INEC) da jami'an tsaro wajen gudanar da sahihin zabe.
Ana shirin gudanar da zabe a Edo
A baya mun ruwaito cewa shirye-shirye sun yi nisa a jihar Edo, yayin da jami'an tsaro, hukumar gudanar da zabe mai zaman kanta ta kasa da yan siyasa ke kokarin ganin an yi zabe cikin nasara.
Baya ga jami'an gwamnati, kungiyoyin fararen hula sun bayyana fargabar cewa akwai kananan hukumomin da za a samu matsalolin tsaro, saboda yan siyasa sun ki sa hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng