'Zai Jawo Maka Matsala:’ An Buƙaci Tinubu Ya Raba Hanya da Buhari tun da wuri

'Zai Jawo Maka Matsala:’ An Buƙaci Tinubu Ya Raba Hanya da Buhari tun da wuri

  • Wata kungiya a Arewacin Najeriya ta bukaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da kar ya bi hanyar Muhammadu Buhari
  • Kungiyar Arewa Think Tank ta kuma ba Bola Tinubu shawara kan harkokin tsaro da inganta tattalin arzikin Najeriya
  • Martanin da Arewa Think Tank ta yi ya biyo bayan maganar da Reuben Abati ya yi ne a kan Muhammadu Buhari kan tsadar rayuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Ƙungiyar Arewa Think Tank ta ba shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu shawara kan tafiyar da mulkin Najeriya.

Shugaban kungiyar, Muhammad Alhaji Yakubu ya ce ya kamata Bola Tinubu ya raba gari da hanyar da Muhammadu Buhari ya bi a lokacin mulkinsa.

Kara karanta wannan

'Ka ba mu kunya:' Shugaban Yarabawa ya tura zazzafar wasika ga Tinubu

Buhari Tinubu
An bukaci Tinubu ya kaucewa tsarin Buhari. Hoto: Muhammadu Buhari| Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa kungiyar ta ce Buhari ya gadarwa Bola Tinubu kasa a rikice, abubuwa sun lalace.

Buƙatar Tinubu ya raba hanya da Buhari

Kungiyar Arewa Think Tank ta bukaci Bola Tinubu ya kaucewa hanyar da Muhammadu Buhari ya bi wajen mulkin Najeriya.

Kungiyar ta ce a lokacin mulkin Buhari an samu cin hanci da rashawa sosai ta yadda aka kama gwamnan CBN da wani dan uwan Buhari wanda hakan ya kawo matsala ga Tinubu.

Arewa Think Tank ta ce dole ne ta ba Bola Tinubu shawara domin kaucewa fadawa irin matsalar da Buhari ya kawo Najeriya a halin yanzu.

An nemi Tinubu ya yaki yan bindiga

Kungiyar Arewa Think Tank ta ce akwai buƙatar shugaban kasa Bola Tinubu ya saka himma wajen yakar yan bindiga.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu: Shugabannin tsaro 15 na Najeriya da jihohin da suka fito

Shugaban kungiyar ya ce hakan na cikin abubuwan da za a tuna Bola Tinubu da shi idan har ya dage ya kawo karshen yan ta'adda.

Muhammad Alhaji Yakubu ya kara da cewa akwai buƙatar gwamnatin Bola Tinubu ta kara mai da hankali wajen samar da abinci a Najeriya.

Matar Tinubu ta raba kudi a Arewa

A wani rahoton, kun ji cewa matar shugaban kasa, Oluremi Tinubu ta raba miliyoyin kudi ga mata a jihar Zamfara domin bunkasa ƙananan sana'o'i.

An ruwaito cewa mata 1,000 ne suka samu kyautar tallafin a wannan karon yayin da matar shugaban kasar ta samu wakilcin matar gwamnan Zamfara.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng