Zaben Kano: Masu Neman Takara 20 a NNPP Sun Fadi Gwajin Kwaya, NDLEA Ta Magantu
- Kimanin masu neman takara a karkashin NNPP a zaben kananan hukumomin Kano ne suka fadi gwajin ta'ammali da miyagun kwayoyi
- Hukumar da ke yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ya bayyana cewa an samu 'yan siyasar suna tu'ammali da wiwi da sauransu
- Wannan na zuwa ne yayin da hukumar zaben Kano ta tsayar da ranar 26 ga watan Oktoba domin gudanar da zaben kananan hukumomin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Hukumar da ke yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) ta kaddamar da gwajin kwayoyi ga masu neman takarar ciyaman da kansiloli a jihar Kano.
An rahoto cewa kimanin ‘yan takara 20 da ke neman mukamai a zaben kananan hukumomi da ke tafe a Kano sun fadi gwajin kwayoyi da hukumar NDLEA ta yi.
Kwamandan NDLEA a jihar, Abubakar Idris Ahmad, ya tabbatar wa jaridar Daily Trust da haka a ranar Talata a ofishinsa.
'Yan takara sun fadi gwajin kwaya a Kano
Ya ce an samu wasu daga cikin masu sha'awar tsayawa takarar suna shan codeine, THC (Tetrahydro, sinadarin da aiki da tabar wiwi, benzodiazenpines da sauransu.
“Ya zuwa yanzu ’yan takara 20 da jam’iyya mai mulki (NNPP) ta gabatar mana a jihar sun fadi gwajin migayun kwayoyi kuma muna ci gaba da atisayen.
"Da yawa daga cikinsu sun fadi gwajin kwayoyi, amma za mu bar hukumar zabe ta yanke shawarar ko sigari kwaya ce saboda ana samun sinadarinta a cikin goro."
- Inji Abubakar Idris.
Kano: Shirin zaben kananan hukumomi
Sai dai shugaban na NDLEA ya ce ya zuwa yanzu babu wata mace da ta aka samu da shan miyagun kwayoyi daga masu neman takarar, inji rahoton The Punch.
Ya yi bayanin cewa ya zuwa yanzu NNPP ce kadai ta gabatar da ‘yan takararta domin yi masu gwajin kwaya kafin mika sunayen 'yan takararta ga hukumar zaben jihar (KANSIEC).
Gwajin kwaya ga masu shirin aure
A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumar da ke yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) ta ce za ta fara yin gwajin kwaya ga masu shirin yin aure a Kano.
Hukumar NDLEA ta bayyana cewa gudanar da gwaji kafin aure zai taimaka wajen gano matsalolin amfani da kwayoyi da hanyar magance su a tsakanin ma'auratan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng