Ana Kuka da Tsadar Fetur, an Fara Tallata Tinubu domin Zaben 2027

Ana Kuka da Tsadar Fetur, an Fara Tallata Tinubu domin Zaben 2027

  • Allunan da ke tallata shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu domin zaɓen 2027 sun fara bayyana a babban birnin tarayya Abuja
  • Allunan waɗanda ke ɗauke da hoton Tinubu da uwargidan gidansa Remi Tinubu sun nuna aniyar shugaban ƙasan na sake tsayawa takara
  • Sai dai Tinubu wanda ya hau kan karagar mulki a ranar, 29 ga watan Mayun 2023 bai fito a hukumance ya nuna zai nemi tazarce be

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Manyan allunan tallata shugaban ƙasa Bola Tinubu domin zaɓen shugaban ƙasa na 2027 sun fara bayyana.

An hango ɗaya daga cikin allunan ne a unguwar Area 1 da ke birnin tarayya Abuja.

Allunan tallata Tinubu sun fara yawo a Abuja
Allunan tallata Tinubu domin zaben 2027 sun fara yawo Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

2027: An fara tallata Bola Tinubu

Kara karanta wannan

Babban alkali ya kubuta daga hannun 'yan ta'adda bayan kwashe watanni a tsare

Jaridar The Punch ta rahoto cewa a allon tallan an rubuta ɓaro-ɓaro aniyar Tinubu ta sake yin tazarce.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A allon wanda ke ɗauke da hoton shugaban ƙasa da matarsa, Remi Tinubu an rubuta 'Grassroots support for Tinubu 2027, initiative 1019'.

Wannan na zuwa ne duk da cewa har yanzu Tinubu bai yi wata sanarwa a hukumance ba game da shirin sake tsayawa takara a zaɓen 2027.

Shugaba Tinubu dai ya hau kan karagar mulki ne a ranar 29 ga Mayu, 2023, inda ya cika burinsa na zama shugaban ƙasa.

Tun bayan hawansa watanni 16 da suka gabata, Shugaba Tinubu ya kawo tsare-tsare waɗanda ƴan Najeriya ke kuka da su musamman cire tallafin man fetur da kuma sakin Naira sakaka.

Karanta wasu labaran kan Tinubu

Kara karanta wannan

Jigon APC ya gayawa Shugaba Tinubu gaskiya kan tsadar rayuwa

Fasto Ayodele ya caccaki Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, Primate Babatunde Elijah Ayodele, ya sake caccakar shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Fasto Ayodele ya soki Shugaba Tinubu ne kan yadda yake kashe kuɗi a gwamnatinsa duk da halin taɓarɓarewar tattalin arziƙin da ake fama da shi a ƙasar nan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng