"PDP Ta Mutu": Ana Rade Radin Haɗaka, Kwankwaso Ya Bugawa Jam'iyyar Kusa a Kai

"PDP Ta Mutu": Ana Rade Radin Haɗaka, Kwankwaso Ya Bugawa Jam'iyyar Kusa a Kai

  • Jigon jam'iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa jam'iyyar PDP a Najeriya ta musu murus gaba daya
  • Kwankwaso ya ce tun lokacin da suka yanke shawarar barin jam'iyyar ta gama lalacewa inda ya sha alwashi kan zaben 2027
  • Legit Hausa ta ji ta bakin wani dan a mutun Atiku Abubakar kan wannan magana ta Rabi'u Kwankwaso game da PDP

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Katsina - Dan takarar shugaban kasa a NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso ya yi magana kan lalacewar PDP.

Sanata Kwankwaso ya ce a yanzu jam'iyyar ta gama mutuwa murus tun bayan ficewarsu daga jam'iyyar.

Kwankwaso ya dira kan PDP yayin da jita-jitar haɗaka tsakaninsu
Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya ce jam'iyyar PDP ta mutu murus. Hoto: Rabi'u Musa Kwankwaso, Atiku Abubakar.
Asali: Facebook

2027: Kwankwaso ya ce PDP ta musu

Kara karanta wannan

2027: Kiran Kwankwaso, Atiku da Obi su tararwa Tinubu ya fusata jam'iyyar APC

Kwankwaso ya fadi haka yayin taron gyara ofishin jam'iyyar NNPP a jiya Asabar 7 ga watan Satumbar 2024 a Katsina, cewar rahoton Punch.

Kwankwaso ya ce sun yanke shawarar barin PDP saboda ta gama mutuwa ba za ta sake tasiri ba.

"Ina mai tunatar da ku cewa PDP ya mutu saboda mun bar jam'iyyar, tun lokacin da suka kauce hanya muka barta."

- Sanata Rabiu Kwankwaso

Kwankwaso ya yi magana kan zaben 2027

Har ila yau, Kwankwaso ya bugi kirji kan zaben 2027 inda ya ce shi zai yi nasara a zaben shugaban kasa da za a yi.

A cewarsa, jam’iyyar a shirye take ta karɓi ragamar shugabancin ƙasa, jihohi da sauran muƙamai a fadin ƙasar nan zuwa 2027.

Kwankwaso ya shawarci al'umma da su guji karbar kyaututtuka a lokacin zabe saboda gudun zaben tumun-dare, Daily Post ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Sanata Kwankwaso ya kadu da ambaliyar ruwa a jihar Borno, ya aika sako

Legit Hausa ta tattauna da masoyin Atiku

Legit Hausa ta ji ta bakin wani dan a mutun Atiku Abubakar kan wannan magana ta Rabi'u Kwankwaso game da PDP.

Kwamred Aliyu Abubakar Abdulkadir ya ce kowa daman ya san Kwankwaso mayaudari ne ba zai yi wata haɗaka ba.

Kwamred Aliyu Dyer ya ce PDP ba tsaransa ba ne saboda yan Najeriya sun gane shi ɗan kwangila ne kuma mayaudari.

Matashin ya ce Najeriya tana dauke da jihohi 36 ba jiha daya ba ce bare ya yi bankaura a kai.

Iliyasu Kwankwaso ya soki hadakar jam'iyyun adawa

A wani labarin, kun ji cewa tsohon kwamishina a Kano, Musa Ilyasu Kwankwaso ya yi magana kan hadakar jiga-jigan jam'iyyun adawa game da zaben 2027

Kwankwaso ya ce Atiku Abubakar da Rabiu Kwankwaso da Peter Obi suna bata lokacinsu ne kan shirin kifar da Bola Tinubu a zabe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.