'Ganduje Zai Bar APC': Malami Ya Yi Hasashen Rikici Tsakanin Tinubu da Shettima

'Ganduje Zai Bar APC': Malami Ya Yi Hasashen Rikici Tsakanin Tinubu da Shettima

  • An yi hasashe Shugaba Bola Tinubu zai fuskanci mawuyacin hali a nan gaba kadan, musamman a shekarar 2025 da ke tunkarowa
  • Primate Elijah Ayodele, ya yi hasashen cewa rikicin siyasa zai kaure tsakanin Tinubu da mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima
  • A cewar malamin, shugaban APC, Abdullahi Ganduje, zai fice daga jam’iyyar, yayin da Godswill Akpabio, shi ma zai yi fada da Tinubu

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

An yi hasashen cewa jam'iyyar APC mai mulki za ta fuskanci musifun siyasa a gabanta yayin da jam'iyyar ke ci gaba da jan ragamar kasar.

Primate Elijah Ayodele, shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, ya yi hasashen rugujewar jam’iyyar APC da matsalolin da Bola Tinubu zai fuskanta.

Kara karanta wannan

Bayan kara kudin mai: Gwamnati ta fadi lokacin da fetur zai wadata a fadin Najeriya

Ayodele ya yi magana kan barin Ganduje jam'iyyar APC da rigima tsakanin Tinubu, Shettima
Ayodele ya hasasho rikici tsakanin Tinubu, Shettima, Akpabio, Tinubu, da sauransu. Hoto: officialABAT, @OfficialAPCNg
Asali: Twitter

Arewa za ta yaki Shugaba Bola Tinubu

Fitaccen malamin addinin ya fitar da wannan hasashen nasa a wani sabon faifan bidiyo da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Alhamis.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Malamin ya bayyana cewa mafi yawan jiga-jigan siyasar Arewa za su kulla kawance domin yakar Shugaba Tinubu da yunkurin tsige shi a zaben shugaban kasa na 2027.

Ya kara da cewa rikicin siyasa mai karfi zai barke tsakanin shugaban kasa da mataimakinsa Kashim Shettima a shekarar 2025.

"Ganduje zai tafi" - Ayodele

A cewar Ayodele, shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, shi ma zai samu matsala da Shugaba Tinubu, kuma zai iya kulla alaka da Abdullahi Ganduje mai barin gado.

"Tinubu da Shettima za su yi fada, rigima mai tsanani kuma hakan zai jawo matsala ga Tinubu. Kuma Akpabio da Tinubu za su yi fada domin Ganduje zai tafi."

Kara karanta wannan

Dattawan Yarabawa sun yi adawa da karin kudin fetur, sun aika sako ga Tinubu

- Inji Ayodele.

Wannan sabon hasashen na Ayodele na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta kiraye-kirayen a tsige Ganduje a matsayin shugaban jam’iyyar APC na kasa, musamman daga shiyyar Arewa ta tsakiya.

APC ta karyata shirin korar Ganduje

A wani labarin, mun ruwaito cewa Sakataren APC na kasa, Sanata Ajibola Basiru ya yi watsi da rade-radin da ake yi cewa jam’iyyar na shirin tsige Abdullahi Ganduje daga shugabanta na kasa.

APC ta nuna kwarin guiwarta ga shugabancin Ganduje yayin da ta bayyana cewa a yanzu babu wata baraka a cikin jam'iyyar tana mai yin godiya ga Shugaba Bola Tinubu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.