Ministan Tinubu Ya Shiga Matsala bayan Ya Yiwa Wasu Gwamnoni Barazana
- Kungiyar NUF ta Arewa maso Gabas ta yi Allah wadai da abin da Ministan Abuja ya yi wanda ta kira da dabancin siyasa
- Ƙungiyar ta ce barazanar da Wike ya yi wa gwamnonin PDP kwanan nan ta tona asirin munanan ɗabi'unsa da rashin ladabi
- NUF ta yi ikirarin Wike ya fita hayyacinsa kuma ya kamata PDP da shugaban ƙasa Bola Tinubu su ɗauki mataki a kansa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Maiduguri, Borno - Ƙungiyar haɗin kan Arewa maso Gabas (NUF) ta buƙaci shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya gaggauta tsige ministan Abuja, Nyesom Wike.
A cewar ƙungiyar bai kamata a ɗauki lamarin barazanar da Wike ya yiwa gwamnonin jam'iyyar PDP da wasa ba domin ba abin da za a lamunta ba ne.
NUF ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ta fitar a Maiduguri, babban birnin jihar Borno, kamar yadda Tribune Nigeria ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wace barazana ministan Abuja ya yi?
Wannan dai na zuwa ne bayan ministan Abuja ya caccaki gwamnonin PDP waɗanda suka nuna goyon baya ga Gwamna Similanayi Fubara a rikicin siyasar Ribas.
Da yake jawabi bayan kaɗa kuri'a a zaben shugabannin PDP a Ribas, Wike ya yi barazanar kunno wa gwamnonin wuta a jihohinsu idan suka shiga rigimar.
Kalaman Wike dai sun ta da ƙura a fagen siyasar Najeriya, inda jam'iyyar PDP ta ce ba za ta bar lamarin ya wuce haka sakaka ba.
NUF ta bukaci Tinubu ya sauke Wike
Jaridar Blueprint ta tattaro cewa yayin da take martani kan lamarin, ƙungiyar NUF ta ce:
"Kalaman Wike cewa duk gwamnan da ya tsoma baki a harkokin siyasar Ribas ba zai iya barci a jiharsa ba suna da haɗari.
"Wannan ya sa kungiyar NUF take rokon a gaggauta sauke Wike daga matsayin ministan babban birnin tarayya Abuja.
“Abin da ya aikata ya nuna bai cancanta ya rike wani mukami a gwamnati ba, ballantana ma wanda ya kai matsayin ministan babban birnin tarayya”.
Gwamnonin PDP sun yi martani
A wani rahoton kuma, gwamnonin jam'iyyar PDP sun yi martani kan kalaman da ministan babban birnin tarayya Abuja Nyesom Wike ya yi.
Ƙungiyar gwamnonin a wata sanarwa ta bayyana kalaman tsohon gwamnan Rivers a matsayin waɗanda ba su dace ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng