“Hadama ba Za Ta Barsu ba”: Kwankwaso kan Hadakar Atiku da ’Yan Adawa a 2027
- Tsohon kwamishina a jihar Kano, Musa Ilyasu Kwankwaso ya yi magana kan hadakar jiga-jigan jam'iyyun adawa game da zaben 2027
- Kwankwaso ya ce Atiku Abubakar da Rabiu Kwankwaso da Peter Obi suna bata lokacinsu ne kan shirin kifar da Bola Tinubu
- Wannan na zuwa ne yayin da jiga-jigan jam'iyyun adawa suke shirin haɗaka ta musamman domin shirin zaben 2027 mai zuwa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Jigon jam'iyyar APC a jihar Kano ya yi magana kan hadakar Atiku Abubakar da Peter Obi da Rabiu Kwankwaso.
Musa Ilyasu Kwankwaso ya ce duka bata lokacinsu suke yi wurin hadaka saboda zaben 2027 mai zuwa.
2027: Kwankwaso ya magantu kan jam'iyyun adawa
Kwankwaso ya bayyana haka ne ga yan jaridu a yau Talata 3 ga watan Satumbar 2024, cewar rahoton Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jigon na APC ya ce babu inda tafiyar za ta je duba da yadda suka yi a baya da kuma hadamar kowa a cikinsu.
Ya ce tarihi zai maimaita kansa ne saboda a baya sun hadu amma da yake kowa yana da haɗama da buri tafiyar ba ta je ko ina ba.
"An yi irin wannan haɗaka amma ta tarwatse saboda kowa yana da burukansa da mugun haɗama."
"A cikinsu babu wanda zai iya janyewa wani saboda yawan buri da kuma son kai da suke da shi."
- Musa Ilyasu Kwankwaso
Kwankwaso ya bugi kirji kan nasarar Tinubu
Kwankwaso ya ce yana da tabbacin Bola Tinubu zai samu nasara a karo na biyu saboda ayyukan alheri da ake yi.
Jigon APC ya ce tabbas haka zai zama cikin sauki saboda samun goyon baya da al'umma ke ba jam'iyyar.
Kwankwaso ya fadi mai daukar nauyin zanga-zanga
Kun ji cewa jigon jam’iyyar APC a jihar Kano, Musa Ilyasu Kwankwaso ya yi magana kan rikicin da aka samu a jihar sakamakon zanga-zanga.
Iliyasu Kwankwaso ya yi kira ga Bola Tinubu da ya ɗorawa Gwamna Abba Kabir Yusuf alhaki kan ɓarna da asarar rayuka da dukiyoyi.
Ya yabawa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso bisa gargadi da kuma kira da ya yi na kada mutane su fito kan tituna domin yin zanga-zanga.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng