An Fadi Dalilin da Ya Kamata Ya Sanya PDP Ta Hukunta Ministan Tinubu

An Fadi Dalilin da Ya Kamata Ya Sanya PDP Ta Hukunta Ministan Tinubu

  • Ƙungiyar NUF ta buƙaci jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya da ta hukunta ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike
  • A cikin wata sanarwa, ƙungiyar ta bayyana cewa ya kamata PDP ta hukunta Nyesom Wike domin dawo da ɗa'a a cikin jam'iyyar
  • Ta ce barazanar da tsohon gwamnan ya yi ga gwamnonin PDP masu goyon bayan Simi Fubara, barazana ce ga zaman lafiyar ƙasar nan

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ƙungiyar North East Unity Forum (NUF) ta buƙaci PDP ta hukunta ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike.

Ƙungiyar ta buƙaci shugabannin jam’iyyar PDP da su hukunta Nyesom Wike domin dawo da ɗa’a a cikin jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Gwamnonin PDP sun fusata da kalaman Wike, sun hada shi da jami'an tsaro

An bukaci PDP ta hukunta Wike
Kungiyar NUF ta bukaci PDP ta hukunts Wike Hoto: Nyesom Ezenwo Wike - CON, GSSRS
Asali: Facebook

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar Abubakar Kabir, ya fitar a ranar Talata, cewar rahoton jaridar The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wace shawara aka ba jam'iyyar PDP?

Ƙungiyar ta jaddada cewa jam’iyyar za ta iya dawo da martabarta ne kawai ta hanyar ɗaukar mataki kan tsohon gwamnan jihar Rivers, wanda ta bayyana a matsayin “ɗan siyasa mai son kai".

Ƙungiyar ta NUF ta ce barazanar da Wike ya yi ta kunna wuta a jihohin gwamnonin da ke goyon bayan Gwamna Fubara ba sakaci ba ne kawai, har ma da barazana ga zaman lafiyar ƙasar nan, rahoton jaridar Independent ya tabbatar.

Meyasa ƙungiyar ke so a hukunta Wike?

Ƙungiyar ta bayyana cewa kalaman nasa sun nuna cewa bai cancanci yana riƙe da wani muƙami a cikin gwamnati ba.

“Saboda haka, NUF ta buƙaci a gaggauta korar Nyesom Wike a matsayin ministan birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

APC ta samu gagarumar nasara a zaben kananan hukumomin jihar Kebbi

"Abubuwan da ya yi sun nuna cewa bai cancanta ya riƙe wani mukami na gwamnati ba, ballantana wanda ya kai ministan Abuja."
"Hakazalika, dole ne shugabannin jam’iyyar PDP su hukunta Wike domin dawo da ɗa’a da tsari a cikin jam’iyyar."
"Ta yin haka, jam’iyyar za ta mutunta tsarin dimokuradiyya, haɗin kai, da biyayya waɗanda su ne ginshiƙin kowane tsarin siyasa."

- Abubakar Kabir

Ƙaranta wasu labaran kan Wike

Wike ya magantu kan sasantawa da Fubara

A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya yi magana kan rikicinsa da Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers.

Wike ya yi watsi da yiwuwar sasantawa tsakaninsa da gwamnan wanda ya gaje shi wajen rike madafun ikon jihar mai arziƙin man fetur.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng