Cikakken Jerin Jihohin da Za a Gudanar da Zabe a Watan Satumba
- Jihohin Edo, Kwara da Anambra su ne jihohi uku da za a gudanar da zaɓe a Najeriya a cikin watan Satumban 2024
- A jihar Edo al’ummar jihar za su fito kaɗa ƙuri’a domin zaɓen sabon gwamna tsakanin jam’iyyar PDP mai mulki da jam’iyyun adawa na APC da Labour Party
- Za kuma a gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a jihar Anambra dake yankin Kudu maso Gabas da kuma jihar Kwara dake yankin Arewa ta Tsakiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Aƙalla jihohi uku ne za su gudanar da zaɓuɓɓuka a Najeriya a cikin watan Satumban 2024.
Zaɓuɓɓukan dake tafe sun haɗa da na ƙananan hukumomi zuwa zaɓen gwamna a jihar Edo.
Gwamnonin jihohi da dama sun fara gudanar da zaɓuɓɓukan ƙananan hukumomi biyo bayan hukuncin da Kotun Ƙoli ta yanke kan cin gashin kan ƙananan hukumomi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jihohin da za a yi zaɓe a watan Satumba
Ga jerin jihohin da za a yi zaɓe a watan Satumba na 2024:
Zaɓen gwamnan jihar Edo
Al'ummar jihar Edo za su fito domin zaɓen sabon gwamna a ranar, 21 ga watan Satumban 2024, kamar yadda hukumar zaɓe ta INEC ta tsara.
Ƴan takarar da ke kan gaba a zaɓen sun haɗa da Asue Ighodalo na jam’iyyar PDP, Sanata Monday Okpebolo na jam’iyyar APC da Olumide Akpata na jam’iyyar Labour Party.
Hakazalika, hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta bayyana cewa an karɓi katunan zaɓe 125,928 daga cikin sababbin katunan zaɓe na dindindin 184,438 a jihar Edo.
Zaɓen ƙananan hukumomi a Anambra
Gwamnatin jihar Anambra ƙarƙashin jagorancin Gwamna Charles Chukwuma Soludo, ta shirya gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a ranar Asabar, 28 ga watan Satumban 2024.
Zaɓen na zuwa ne shekara 10 bayan an yi zaɓen ƙananan hukumomi a jihar wacce ke a yankin Kudu maso Gabas na Najeriya.
Shugabar hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Anambra (ANSIEC), Genevieve Osakwe, ta bayyana cewa ana shirye-shiryen gudanar da zaɓen ba tare da wata tangarɗa ba.
Zaɓen ƙananan hukumomi a Kwara
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Kwara (KWSIEC) ta bayyana cewa za ta gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a jihar a ranar 21 ga watan Satumba, cewar rahoton jaridar The Punch.
A cewar sanarwar da hukumar ta fitar, ana ƙoƙarin ganin an gudanar da zaɓen a ranar da aka tsara.
Jam'iyyar APC ta lashe zaɓe a Kebbi
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam’iyyar APC ta lashe dukkanin kujerun shugabannin ƙananan hukumomi 21 da Kansiloli 225 a jihar Kebbi.
A ranar Asabar, 31 ga watan Agustan 2024 hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Kebbi (KESIEC) ta gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a faɗin jihar.
Jam'iyyar APC mai mulki a jihar ta lashe dukkanin kujeru a zaɓen wanda aka fafata tsakanin jam'iyyun siyasa 17.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng