Kano: Malaman Musulunci Sun Watsar da Tafiyar Abba, Sun bi Barau a APC
- Kungiyar malaman addinin Musulunci da alarammomi ta fice daga jami'yyar NNPP mai mulki a jihar Kano zuwa APC
- Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ne ya karbi tawagar kungiyar a babban birnin tarayya Abuja
- Sanata Barau Jibrin ya bayyana cewa zai shirya taron gasar Alkur'ani mai girma a Kano domin haɓaka ilimin addinin Musulunci
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Kungiyar malaman addinin Musulunci da makaranta Alkur'ani a jihar Kano sun fita daga tafiyar Abba Kabir Yusuf.
Mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Barau Jibrin ne ya karɓi yan kungiyar zuwa jam'iyyar APC a Abuja.
Legit ta tatttaro bayanai kan yadda aka karbi malaman ne a cikin wani sako da Sanata Barau Jibrin ya wallafa a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Malaman addini sun koma APC a Kano
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ya karbi tawagar malaman addini da makaranta Alkur'ani zuwa APC.
Malaman sun fito ne daga yankunan Kano ta Tsakiya da Kano ta Kudu kuma. sun fita ne daga NNPP mai kayan marmari zuwa APC.
Barau Jibrin zai shirya gasar Alkur'ani
Bayan karɓar malaman, Sanata Barau Jibrin ya bayyana cewa zai shirya gasar karatun Alkur'ani mai girma a Kano.
Sanatan ya ce za a shirya gasar karatun Alkur'anin ne a karkashin gidauniyar Barau Jibrin kuma domin yada ilimi za a yi gasar.
Ƙoƙarin da Tinubu yake yi a Arewa
Haka zalika Barau Jibrin ya bayyana wa malaman cewa cikin kokarin Bola Tinubu ne aka samar da hukumar cigaban Arewa maso yamma.
A karkashin haka ya yi kira ga malaman kan cigaba da yi wa shugaban kasa Bola Tinubu addu'ar samun nasara.
Matasan NNPP sun sauya sheka a Kano
A wani rahoton, kun ji cewa shugabannin matasan jam'iyyar NNPP mai mulki a jihar Kano sun sauya sheka zuwa jami'yyar APC mai adawa.
An ruwato cewa matasan sun bayyana sauya shekar ne yayin ganawa da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng