Ministan Buhari Ya Yi Nadamar Shiga APC? Na Kusa da Tsohon Gwamnan Ya Magantu

Ministan Buhari Ya Yi Nadamar Shiga APC? Na Kusa da Tsohon Gwamnan Ya Magantu

  • Tsohon gwamnan Rivers, Rotimi Amaechi ya yi martani bayan yada jita-jitar cewa yana nadamar shiga jam'iyyar APC
  • Na hannun daman tsohon Ministan, Eze Chukwuemeka Eze shi ya bayyana haka inda ya karyata rahoton da ake yadawa
  • Eze ya yi martanin ne yayin da ake yada cewa tsohon Ministan ya yi nadamar shiga APC saboda yadda aka watsar da shi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Tsohon Ministan Sufuri a Najeriya, Rotimi Amaechi ya musanta cewa ya yi nadamar shiga APC.

An yada wasu rahotannin da ke cewa Amaechi bai jin dadin yadda aka nuna masa wariya daga jam'iyya mai mulkin kasa.

Kara karanta wannan

Hadimin Abdullahi Ganduje ya fadi 'tuggun' da aka shiryawa jam'iyyar APC

Na kusa da tsohon Minista ya yi magana kan rahoton da ake yadawa na yin nadamar shiga APC
Na hannun daman Rotimi Amaechi ya karyata labarin cewa tsohon Ministan ya yi nadamar shiga APC. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Rt Hon Chibuike R Amaechi.
Asali: Facebook

Gaskiya kan labarin nadamar shigar Amaechi APC

Jigon APC, Cif Eze Chukwuemeka Eze ya karyata rahoton da ake yadawa kan tsohon Ministan, cewar rahoton Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Eze ya ce Amaechi bai taba yin hira ta musamman da wanda ya ke yada labarin cewa ya yi nadamar shiga APC ba.

Na kusa da Amaechi ya tabbatar da cewa Amaechi bai taba nadamar shiga jam'iyyar ba, kamar yadda Daily Post ta kawo rahoto.

Amaechi ya ba da gudunmawa a gina APC

Cif Eze ya ce mai gidan nasa ya ba da gudunmawa wurin gina APC inda ya ce rashin shugabanci mai kyau ba iya jam'iyyar ba ne kadai illa kasa baki daya.

Jigon jam'iyyar ya ce tsohon Ministan kamar sauran 'yan Najeriya yana jin bakin ciki musamman kan halin kunci da ake ciki.

Ya ce saboda Amaechi ya yi shiru ba shi ne yana nadamar shiga APC ba inda ya ce ya dauki matakin yin shiru ne kan lamuran kasar a karan kansa.

Kara karanta wannan

Abba ya sa tsoho sharba kuka a gidan gwamnati, Allah ya amsa addu’ar dattijo

Jam'iyyar APC ta magantu kan ficewar Amaechi

Kun ji cewa shugabannin jam’iyyar APC a jihar Ribas ba su da tabbas game da jam'iyyar da Rotimi Amaechi yake ciki a halin yanzu.

Tony Okocha, shugaban kwamitin riko na jam'iyyar a Rivers, ya ce tsohon gwamnan ya nesanta kansa da APC.

Okocha ya yi ikirarin cewa Amaechi ne da kansa ya gargadi shugabannin APC da ka da su sake aika masa da takardar gayyata.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.