"Wike ba Zai Zama Mana Kadangaren Bakin Tulu ba," PDP Ta Fadi Dalilin Kafa Kwamitin Ladabtarwa

"Wike ba Zai Zama Mana Kadangaren Bakin Tulu ba," PDP Ta Fadi Dalilin Kafa Kwamitin Ladabtarwa

  • PDP ta kafa kwamitoci guda biyu domin duba halin da jam'iyyar ke ciki da zimmar farfado da ita gabanin zaben 2027
  • Guda daga cikin kwamitocin zai duba yadda za a sasanta rigingimun da jam'iyyar ke fuskanta a matakai daban-daban
  • Mataimakin sakataren yada labaran PDP, Barista Ibrahim Abdullahi ya shaidawa Legit kwamitin zai binciki wasu 'yan jam'iyyar

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Jam'iyyar PDP ta bayyana kafa wasu kwamitoci guda biyu da za su duba halin da jam'iyyar ke ciki domin daukar matakan gyara kafin kakar zaben 2027.

Mataimakin sakataren yada labaran jam'iyyar na kasa, Barista Ibrahim Abdullahi bayyana cewa aikin daya daga cikin kwamitocin shi ne gyara alakar dake tsakanin 'yan PDP.

Kara karanta wannan

Hadimin Abdullahi Ganduje ya fadi 'tuggun' da aka shiryawa jam'iyyar APC

Nyesom
PDP za ta ladabtar da Nyesom Wike Hoto: Nyesom Ezenwo Wike - CON, GSSRS
Asali: Facebook

Barista Ibrahim ya shaidawa Legit cewa an kafa daya kwamitin domin ya tuhumi wasu daga cikin 'ya'yan jam'iyyar da ake zargi da cin amanar jam'iyya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daya daga cikin wadanda za a bincika shi ne Ministan Abuja, Nyesom Wike, wanda Barista Ibrahim Abdullahi ya zarga da kokarin rikewa jam'iyyar makogaro.

"Gwara PDP ta rasa Wike," Barista Ibrahim

Mataimakin sakataren yada labaran PDP, Barista Ibrahim Abdullahi ya bayyana cewa akwai yan jam'iyyar da dama da ake zargi da yi masu zagon kasa.

Ya bayyana cewa ko a zaben 2023, an yi zargin Ministan Abuja, Nyesom Wike da yi wa dan takarar PDP a wancan lokaci, Atiku Abubakar makarkashiyar faduwa zabe.

Jaridar Punch ta wallafa cewa PDP za ta tuhumi Wike da sauran wadanda ake zargi da yi wa PDP zagon kasa, kuma gwara a ce Wike ya bar jam'iyyar da ya jawo masu matsala a zaben gaba.

Kara karanta wannan

Tinubu zai shiga matsala: An gano shirin Atiku, Obi, Kwankwaso na hade kansu a 2027

Wike ya yi wa gwamnonin PDP barazana

A baya kun ji cewa Ministan Abuja, Nyesom Wike ya yi barazana ga sauran gwamnonin PDP da ke fadin kasar nan idan su ka sake tsoma bakinsu a cikin rikicinsa da gwamna Siminalayi Fubara.

Mista Wike wanda ya nanata cewa ba zai bar PDP ba, ya kara da cewa ya san makamar siyasar dukkanin jihohin PDP, kuma idan ba su fuskanci matsalolin gabansu ba, zai jawo masu matsala.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.