“Ban da Osinbajo”: Sule Lamido Ya Fadi Ainihin Wanda Buhari Ya So Ya Gaje Shi
- Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido ya bayyana wanda Muhammadu Buhari ya so ya gaje shi a zaben shugaban kasa.
- Lamido ya ce Buhari bai so Bola Tinubu ba tun farko inda ya ce hatta mataimakinsa, Yemi Osinbajo bai aminta da shi ba
- Tsohon gwamnan ya ce Buhari ya so tsohon shugaban Majalisar Dattawa, Ahmed Lawan wanda dan Arewa ne ya gaje shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Jigawa - Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido ya ce tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari bai so Bola Tinubu ba tun farko.
Sule Lamido ya ce Buhari ya so tsohon shugaban Majalisar Dattawa, Ahmed Lawan ya gaje shi.
Lamido ya fadi kuskuren Buhari a 2023
Tsohon Ministan ya bayyana haka yayin hira da Tribune da aka wallafa a jiya Asabar 31 ga watan Agustan 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Lamido ya ce Buhari bai yi lissafi mai kyau ba a siyasa inda ya so dan Arewa ya gaje shi bayan shafe shekaru takwas a kan mulki.
Ya ce har ila yau, Buhari bai aminta da mataimakinsa, Yemi Osinbajo ya gaje shi ba saboda wasu dalilai.
Lamido ya fadi wanda Buhari ya so
"Bai so Tinubu ko kadan, akwai wanda ya ke so, hatta mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo Buhari bai aminta da shi ba."
"Ahmed Lawan ya ke so ya gaje shi amma wannan lissafi na shi bai yi kyau ba, ka yi shekaru takwas kana mulki kuma kana bukatar dan Arewa ya sake gadan kujerarka."
"Ba za ka yi haka a Najeriya ba, akwai wasu abubuwa da ba za ka iya sauyawa su ba, ba irin Najeriya ta yau ba a yanzu."
- Sule Lamido
Lamido ya yi magana kan zaben 2027
Mun baku labarin cewa tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido ya yi magana kan zaben 2027 da ke tafe.
Lamido ya ce ba karamin wahala zai yi ga jam'iyyun adawa su iya tumbuke Tinubu a zaben 2027 da ake tunkara ba.
Tsohon gwamnan bayyana Tinubu a matsayin wanda ya kware ya kuma karanci siyasar kasar da bai dogara da kowa wurin zamowa shugaban kasa ba.
Asali: Legit.ng