"Zan Kunno Muku Wuta a Jihohinku," Ministan Tinubu Ya Yiwa Wasu Gwamnoni Barazana
- Nyesom Wike ya mayar da martani ga gwamnonin jam'iyyar PDP waɗanda suka nuna za su shigar wa Gwamna Fubara a rikicin Ribas
- Wike, ministan Abuja ya yi barazanar cewa idan gwamnonin suka sake suka saka kansu a rikicin to zai jefa su cikin matsala a jihohinsu
- Tsohon gwamnna ya ƙara nanata cewa yana nan daram a jam'iyyar PDP, ba zai sauya sheƙa saboda wani mutum ɗaya ba
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Rivers - Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya gargaɗi gwamnonin jam'iyyar PDP su guji tsoma baki a harkokin siyasar jihar Ribas.
Wike, tsohon gwamnan jihar Ribas kuma babban ƙusa a PDP, ya ce ba shi da shirin barin jam'iyyar saboda wani mutum ɗaya.
Ministan ya bayyana hakan ne yayin da yake kaɗa kuri'arsa a zaɓen shugabannin PDP da ya gudana a Fatakwal, babban birnin jihar Ribas, Daily Trust ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wike na shirin karɓe PDP a Rivers
Nyesom Wike ya ce idan aka kammala wannan zaɓe cikin nasara, magoya bayansa sun karɓe ragamar shugabancin PDP a jihar tun da tsagin Fubara sun tsame kansu.
Da yake mayar da martani ga ƙungiyar gwamnonin PDP karkashin Gwamna Bala Mohammed na Bauchi, Wike ya yi barazanar kunna masu wuta a jihohinsu.
Idan baku manta ba a makon jiya, gwamnonin PDP sun nuna goyon baya ga Gwamna Siminalayi Fubara a taron da suka yi a Taraba.
Wike ya caccaki gwamnonin PDP
A rahoton The Cable, Mista Wike ya maida masu martani da cewa:
"Na ji wasu gwamnoni sun ce za su ƙwace ragamar PDP daga hannunmu su ba wani daban, na samu labarin sun ba shi tabbacin za su kwato jam'iyyar nan su damƙa masa.
"Ina tausayin waɗancan gwamnonin domin zan kunno masu wuta a jihohinsu, idan Allah ya baka ni'ima ka yi butulci, ko a Bauchi kake ko ma a ina ne, za ka shiga matsala, kun yi bankwana da zaman lafiya.
2027: Jigon PDP ya ba Atiku mafita
A wani rahoton kuma wani jigo a PDP, Glintstone Akinniyi ya yi bayanin yadda Atiku Abubakar zai iya lashe tikitin takarar shugaban ƙasa a 2027.
Akinniyi ya ce idan Atiku na son takara ya zama tilas ya fito ya nema, inda ya ƙara da cewa jam'iyyu ba su ba mutum takara sai ya nema.
Asali: Legit.ng