Hukuncin Kotun Koli Ya Sa An Matso da Zaben Kananan Hukumomi a Jihar Kano

Hukuncin Kotun Koli Ya Sa An Matso da Zaben Kananan Hukumomi a Jihar Kano

  • Hukumar zaɓe ta jihar Kano ta dawo zaben kananan hukumomi ranar 26 watan Oktoba maimakon 30 ga watan Nuwamba
  • Shugaban KANSIEC, Farfesa Sani Lawal Malumfashi ne ya bayyana haka a wurin taron gaggawar da aka gudanar ranar Jumu'a
  • Ya ce hukumar ta yanke canza ranar zaɓen ne biyo bayan hukuncin kotun ƙoli na ƴancin ƙananan hukumomi a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Kano (KANSIEC) ta dawo da zaɓen kananan hukumomi da aka shirya yi ranar 26 ga watan Oktoba, 2024.

Hukumar KANSIEC ta canza ranar da za a gudanar da zaɓen ciyamomi da kansiloli daga 30 ga watan Nuwamba, 2024 da aka sanar a kwanakin baya.

Kara karanta wannan

Katsina: Kotun ɗaukaka ƙara ta yanke hukuncin ƙarshe kan kujarar ɗan majalisar tarayya

Gwamna Abba Kabir Yusuf.
An ɗaga zaben ƙananan hukumomi na jihar Kano zuwa watan Nuwamba Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Shugaban hukumar, Farfesa Sani Lawal Malumfashi, ne ya sanar da hakan a taron gaggawa na masu ruwa da tsaki ranar Juma’a, Daily Trust ta kawo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa aka ɗage zaɓen ciyamomi a Kano

Farfesa Sani Malumfashi ya ce hukumar ta yanke shawarar matso da zaɓen zuwa watan Oktoba ne sakamakon hukuncin da kotun koli ta yanke na ba kananan hukumomi ƴanci.

Shugaban hukumar KANSIEC ya roƙi jam'iyyun siyasa da sauran masu ruwa da tsaki su fahimci dalilin matso da zaɓen.

A baya dai hukumar KANSIEC ta kayyade Naira miliyan 10 da Naira miliyan 5 a matsayin kudin fom din takarar shugaban ƙaramar hukuma da na kansiloli.

Yadda aka tsara zaɓen kananan hukumomi

Za a fara yakin neman zaben ne daga ranar 1 ga watan Satumba, 2024 yayin da za kuma a fara sayar da fom din tsayawa takara a ranar 16 ga watan Satumba.

Kara karanta wannan

Abba ya samu giɓi ana shirin zabe, shugabannin Kwankwasiyya sun koma APC

A ranar 27 ga watan Satumba ne aka tsara maido da fom da tantance ‘yan takara yayin da jam’iyyun siyasa ke da damar canza ƴan takara har zuwa ranar 18 ga watan Oktoba.

Sani Lawal Malumfashi ya ce za a sanar da sakamakon zaben nan take bayan an kammala kidaya kuri’u, rahoton The Nation.

Wani jigon NNPP a ƙaramar hukumar Nassarawa, Saidu Abdu ya shaidawa Legit Hausa cewa sun riga sun gama shirin zaɓen don haka matso da rana ba zata masu illa ba.

Game da wanda NNPP za ta tsayar a ƙaramar hukumarsa, Saidu ya ce har yanzun ba su yanke ba saboda akwai ɗan ruɗani.

"Mu a nan Nassrawa mutum hudu suka fito takara kuma a maganar gaskiya duk sun cancanta shiyasa har yanzu ba mu yanke wanda za mu marawa baya ba," in ji shi.

Kano: Ƴan Kwankwasiya sun koma APC

A wani rahoton kuma 'yan Kwankwasiyya akalla 6,000 ne suka watsar da tafiyar jam'iyyar NNPP a Kano inda suka koma gidan Sanata Barau I. Jibrin a APC.

Kara karanta wannan

Kaduna: Ambaliyar ruwa ta lalata gidaje sama da 200, SEMA ta ɗauki mataki

Rahotanni sun bayyana cewa 'yan kungiyar 'Na Dikko Dakin Kara' sun ziyarci Sanata Barau har gidansa domin nuna mubayi'arsu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262