Shirin Zaben Ciyamomi Ya Yi Nisa, Hukuma ta Fara Raba Kayan Zabe a Kebbi

Shirin Zaben Ciyamomi Ya Yi Nisa, Hukuma ta Fara Raba Kayan Zabe a Kebbi

  • Yayin da ake shirin zaben kananan hukumomi a ranar Asabar, hukumar zabe ta jihar Kebbi ta yi nisa a shirinta
  • Hukumar zaben (KESIEC) ta bayyana cewa yanzu haka an fara kai kayayyakin gudanar da zaben
  • Ana raba kayayyakin zaben a hedkwatar yan sanda yayin da wakilan jam'iyyu da jami'an tsaro ke sa ido kan rabon

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kebbi - Hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kebbi ( KESIEC) ta bayyana cewa shirye-shiryen gudanar da zaben kananan hukumomin jihar sun yi nisa.

Yanzu haka ana raba kayayyakin zaben a hedkwatar yan sandan jihar, karkashin sa idon wakilan jam'iyyu, jami'an tsaro da gamayyar kungiyar jam'iyyu (IPAC).

Kara karanta wannan

Hukuncin kotun koli ya sa an matso da zaben ƙananan hukumomi a jihar Kano

Nasir
An fara raba kayan zaben kananan hukumomi a Kebbi Hoto: Sarki Yahaya
Asali: Facebook

AIT ta wallafa cewa ana raba kayan ne gabanin zaben kananan hukumomin jihar Kebbi 21 da zai gudana a ranar Asabar, 31 Agusta, 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kowa zai yi zabe a jihar Kebbi?

Yayin da ake raba kayan zaben kananan hukumomi a Kebbi, gwamnati ta bayyana cewa za a tabbata kayan sun isa ko ina a jihar.

Kwamishinan yada labaran jihar, Muhammad Kaura Danhakimi ya ce za a kai kayan kananan hukumomi 21 da Kebbi ke da su, sannan har wadanda ambaliya ya shafa za su yi zabe.

An nemi hadin kan jama'a a zaben Kebbi

Jam'iyyu 17 daga cikin 18 da ake da su a jihar Kebbi ne za su fafata a zaben kananan hukumomin jihar a gobe Asabar bayan PDP ta janye daga zaben.

Gwamnatin jihar ta nemi hadin kan jama'a, jami'an tsaro, yan jarida da jam'iyyu wajen tabbatar da an yi zaben cikin nasara da kwanciyar hankali.

Kara karanta wannan

Kwalliya ta zo da gardama: Budurwa ta sheka lahira a wajen tiyatar karin mazaunai

Gwamnati ta bayar da hutun zabe

A baya mun ruwaito cewa gwamnatin jihar Kebbi ta bayyana ranar Juma'a da ranar hutu ga jama'a domin ba su damar shirya tunkarar zaben kananan hukumomi.

Gwamnan jihar, Dr. Nasir Idris ya shawarci daukacin ma'aikatan jihar da sauran jama'a su fito kwansu da kwarkwararsu domin kada kuri'a a zaben Asabar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.