Ganduje Ya Sanar da Ranar Babban Taron APC, Tinubu da Buhari za Su Halarta
- Shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Umar Ganduje ya ce jam'iyyar za ta gudanar da babban taronta na majalisar zartarwa (NEC)
- Dr. Ganduje ya ce ana sa ran shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da tsohon shugaba Muhammadu Buhari za su halarta
- Ya ce manyan shugabannin biyu za su halarta ne saboda wasu muhimman batutuwa da za a tattauna da suka shafi APC
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Shugaban APC na kasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa za a gudanar da babban taron jam'iyyar a watan Satumba.
Dr. Ganduje ya bayyana cewa za a gudanar da taron NEC a ranar 12 Satumba, 2024, kuma ana sa ran shugaba Bola Tinubu da tsohon shugaba Muhammadu Buhari za su halarci taron.
Arise TV ta wallafa cewa Abdullahi Ganduje ya ce ana sa ran dukkanin gwamnonin APC za su halarci taron saboda muhimmancinsa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me za a tattauna a taron APC NEC?
Duk da Dr. Abdullahi Umar Ganduje bai bayyana takamaiman abubuwa da za a tattauna a babban taron ba, amma ya ce batutuwa ne masu muhimmanci.
Shugaban ya shaidawa manema labarai a Kano cewa muhimmacin abubuwan da za a tattauna ne ya sa jagororin jam'iyyar za su halarci taron, This day ta wallafa labarin.
Shirin jam'iyyar APC kan Zabuka
Shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa akwai alamun samun nasara a zaben gwamnoni da za a gudanar a jihohin Edo da Ondo.
Ya ce duk da rasa kujerar gwamna da suka yi a baya saboda rikicin cikin gida a Edo, sun yi kyakkyawan shirin kwato jihar.
APC na shirye-shirye karbe jihohi
A wani labarin kun ji cewa shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Umar Ganduje ya ce su na kokarin zamanantarwa da tattara bayanan yan jam'iyya da ke jihohi.
Dakta Ganduje ya kara da cewa su na shirin tattara bayanan yan jam'iyya domin yi masu rajista ta yanar gizo, yayin da ake kokarin hade kansu wuri guda.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.\
Asali: Legit.ng