Tafiyar Kwankwasiyya Ta Samu Matsala a Kano, Fiye da Mutane 6000 Sun Sauya Sheka

Tafiyar Kwankwasiyya Ta Samu Matsala a Kano, Fiye da Mutane 6000 Sun Sauya Sheka

  • 'Yan Kwankwasiyya akalla 6,000 ne suka watsar da tafiyar jam'iyyar NNPP a Kano inda suka koma gidan Sanata Barau I. Jibrin
  • Rahotanni sun bayyana cewa 'yan kungiyar 'Na Dikko Dakin Kara' sun ziyarci Sanata Barau har gidansa domin nuna mubayi'arsu
  • Sanata Barau ya yi wa 'yan kungiyar maraba da zuwa APC, inda ya sha alwashin share masu hawayen da NNPP ta gaza share masu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I Jibirin ya karbi 'yan kungiyar 'Na Dikko Dakin Kara' da suka koma jam'iyyar APC.

Kungiyar 'yan asalin Katsina mazauna Kano bisa jagorancin Alhaji Usman Abdullahi Masari sun sanar da ficewarsu daga tafiyar Kwankwasiyya.

Kara karanta wannan

Kwalliya ta zo da gardama: Budurwa ta sheka lahira a wajen tiyatar karin mazaunai

Sanata Barau ya karbi 'yan Kwankwasiyya da suka sauya sheka zuwa APC
'Yan Kwankwasiyya 6,000 sun sauya sheka zuwa APC a Kano. Hoto: Barau I. Jibrin
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa 'yan kungiyar sun je gidan Sanata Barau da ke Abuja domin yin mubayi'a ga tafiyarsa da kuma jam'iyyar APC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Barau ya yi godiya da shigowa APC

Bayan karbar wadanda suka sauya shekar, Sanata Barau ya jinjina masu kan wannan tunani da suka yi na komawa APC inda ya yi alkawarin ba su kulawa kamar kowa.

Sanata Barau ya wallafa hotunan wannan taron a shafinsa na Facebook, inda ya bayyana cewa:

"Muna muku maraba da shigowa wannan tafiya ta mu ta APC. Ina mai tabbatar muku cewa daga yau mun zama ɗaya, kuma zamu baku kulawa kamar sauran ýan jam'iyya."
"Mun saurari korafe-korafenku. Ina mai ba ku tabbacin cewa kunzo inda za a share maku hawaye. Ina matukar godiya da wannan ziyarar da kuka kawo mun."
"Sannan ina miƙa godiya ga wannan ƙungiya mai albarka bisa karrama ni da su kayi da lambar yabo kan ƙoƙarinmu na samar da Hukumar Raya Yankin Arewa maso Yamma."

Kara karanta wannan

Abba ya samu giɓi ana shirin zabe, shugabannin Kwankwasiyya sun koma APC

Kwankwasawa 6,000 sun koma jam'iyyar APC

Tun da fari, shugaban kungiyar, Alhaji Usman Abdullahi Masari ya koka da yadda aka yi musu rashin adalci a jam’iyyar da suka baro ta NNPP.

Alhaji Masari ya ce:

“Kano ta yi mana komai, kuma ba za mu taba mantawa da jihar ba. Amma mun shiga Kwankwasiyya ba tare da sanin Sanata Barau shi ne mutumin da ya dace mu bi ba.
"A yau gamu gaba gare ka, kafatanin 'yan kungiyarmu da suka haura mutum 6,000, mun ajiye tafiyar Kwankwasiyya mun dawo APC."

Duba hotunan taron a nan kasa:

'Yan APC 1000 sun koma NNPP

A wani labarin kuma, mun ruwaito cewa dubunnan magoya bayan jam'iyyar APC a jihar Kano sun watsar da tafiyar Abdullahi Ganduje sun koma NNPP.

An ce masu sauya sheƙar sun samu tarba a gidan gwamnati inda shugaban jam'iyyar NNPP na Kano ya yi maraba da zuwansu jam'iyya mai mulkin jihar.

Kara karanta wannan

Ganduje ya tafka asara, daruruwan 'yan APC sun watsar da ita ana daf da zabe

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.