Ganduje Ya Girgiza 'Yan Adawa, Ya Fadi Shirin APC Na Kwace Jihohin Najeriya
- Shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya yi bayyana cewa jam'iyyar na shirin ganin jihohin Najeriya 36 sun dawo hannunta
- Ganduje ya nuna ƙwarin gwiwar cewa APC za ta lashe zaɓukan gwamna a jihar Ondo da Edo waɗanda za a yi a wannan shekarar
- Shugaban na APC ya yi nuni da cewa suna shirin karɓo jihar Anambra daga hannun jam'iyyar APGA a zaɓen gwamnan na 2025
- Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
FCT, Abuja – Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi magana kan zaɓukan gwamnonin da ke tafe.
Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya nuna ƙwarin gwiwar cewa jam’iyyar APC za ta karɓe dukkanin jihohin Najeriya 36 idan ta cimma burinta.
Abdullahi Ganduje ya faɗi shirin APC
Ganduje ya bayyana haka ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin shugabannin ƙungiyar ƴan jarida ta ƙasa (NUJ) reshen jihar Kano a ranar Alhamis, cewar rahoton jaridar The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Na yi amanna cewa yaƙin neman zaɓenmu yana tafiya yadda ya dace, muna shirin tunkarar wannan zaɓen kuma mun yi imanin cewa za mu iya ƙwato jihar mu (Edo)."
"Saboda jiha ce ta APC amma saboda rikicin cikin gida mun rasa ta a hannun PDP amma muna da tabbacin za mu ƙwato jihar."
"Ga Ondo, dama jihar APC ce kuma lokacin da tsohon gwamnan ya rasu, ya bar matsaloli da dama, amma mun samu damar magance waɗannan matsalolin."
- Abdullahi Umar Ganduje
APC na shirin ƙwace jihohin Najeriya
Ganduje ya bayyana cewa idan APC ta lashe zaɓen jihar Edo, jam'iyyar za ta koma tana da jihohi 21 cikin 36 na ƙasar nan, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.
Shugaban na APC ya bayyana cewa suna shirin ganin jihar Anambra ta dawo hannun APC a zaɓen gwamnan da za a yi a shekara mai zuwa.
Ganduje ya kuma yi nuni da cewa suna shiri domin ganin sun samu ƙarin jihohi daga yankin Kudu maso Gabashin Najeriya.
Karanta wasu labaran kan APC
- Babbar kotu ta ƙara jiƙawa Ganduje aiki kan korar wasu shugabannin APC
- Abba ya samu giɓi ana shirin zabe, shugabannin Kwankwasiyya sun koma APC
- Rikicin APC ya dauki zafi bayan an dakatar da shugabannin jam'iyya
Jigon APC ya fice daga jam'iyyar
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mai binciken kuɗin APC na ƙasa, Cif George Moghalu, ya yi murabus daga jam’iyyar a hukumance.
Tsohon shugaban na hukumar NIWA ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar ne a cikin wata wasiƙa da ya aikawa shugabanninta.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng