Atiku Ya Fadi Babban Abin da Ya Dame Shi Bayan Jigon PDP Ya Caccake Shi

Atiku Ya Fadi Babban Abin da Ya Dame Shi Bayan Jigon PDP Ya Caccake Shi

  • Atiku Abubakar ya yi wa jigon PDP martani bayan ya ba shi shawarar ya haƙura da yin takara a zaɓen shekarar 2027 mai zuwa
  • Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana cewa halin da gwamnatin Tinubu ta jefa ƴan Najeriya ne a ransa ba tunanin 2027 ba
  • Ya shawarci Bode George da ya mayar da hankali wajen ba Tinubu shawarar yadda za a ceto ƴan Najeriya ba siyasar 2027 ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa abin da ya dame shi a halin yanzu shi ne halin da ƴan Najeriya suke ciki.

Atiku Abubakar ya bayyana cewa a yanzu ba tunanin zaɓen shekarar 2027 ba ne a ransa.

Kara karanta wannan

Tsohon kakakin kamfen Atiku ya faɗi ƴan siyasar da ke rura wutar rashin tsaro a Najeriya

Atiku ya caccaki Bode George
Atiku ya yiwa Bode George martani Hoto: Atiku Abubakar, Bode George
Asali: Facebook

Atiku ya yi martani ne kan shawarar da ɗaya daga cikin ƴan kwamitin amintattun na PDP, Cif Bode George, ya ba shi ta ya haƙura da yin takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Atiku Abubakar ya caccaki jigon PDP

Martanin na Atiku Abubakar na cikin wata sanarwa ne wacce mai magana da yawun bakinsa, Paul Ibe, ya ba jaridar Vanguard.

"A halin yanzu abin da ke ran Atiku Abubakar bai shafi 2027 ba. Abu ne da ya shafi 2025 da 2026 da bayan nan. Abin da ya dame shi halin da wannan gwamnatin ta jefa ƴan Najeriya a ciki."
"Rashin sanin ya kamata ne a riƙa magana kan 2027 a yanzu lokacin da wanda aka zaɓa a 2023 bai amfani ƴan Najeriya da komai ba, waɗanda aka ƙara jefa rayuwarsu cikin mawuyacin hali ta kowace fuska."

Kara karanta wannan

'Dalilin da ya sa Atiku, Kwankwaso da Obi ba ba su iya kayar da Tinubu a 2027 ba'

"Kamata ya yi Bode George ya mayar da hankalinsa wajen ba Tinubu shawara ya sake duba manufofinsa waɗanda suka ƙara zurfafa talauci da rarrabuwar kawuna a ƙasar mu, maimakon mayar da hankali kan siyarar 2027."

- Atiku Abubakar

Atiku ya soki mulkin Bola Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya zargi shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da kokarin lalata kasar nan.

Haka kuma Atiku Abubakar na ganin iyalan shugaba Tinubu da abokansa na kokarin cefanar da kasar nan gabanin kammala wa'adinsa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng