Jam'iyyar Adawa Ta Dakatar da Ɗan Majalisar Tarayya Mai Ci, Ta Jero Dalilanta
- Dan Majalisar Tarayya a jihar Lagos ya shiga matsala bayan jam'iyyarsa ta LP mai adawa a Najeriya ta dakatar da shi
- Jam'iyyar ta dakatar da Hon. Seyi Sowunmi mai wakiltar mazabar Ojo a jihar har na tsawon watanni uku masu zuwa
- LP na zarginsa da kin mutunta gayyatar da ta yi masa gaban kwamitin ladabtarwa, ta ce hakan zagon kasa ne da raini
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Lagos - Jam'iyyar adawa ta LP ta dakatar da dan Majalisar Tarayya mai ci a jihar Lagos.
Jam'iyyar LP ta dauki matakin ne kan Seyi Sowunmi da ke wakiltar mazabar Ojo har na tsawon watanni uku masu zuwa.
LP ta dakatar da dan Majalisar Tarayya
Shugaban jam'iyyar a jihar Lagos, Oluwanifemi Elegbede shi ya tabbatar da haka a yau Laraba 28 ga watan Agustan 2024, cewar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Elegbede ya ce an dakatar da Sowunmi ne bayan kin bin umarnin jam'iyyar da ta gayyace shi.
Sowunmi ya ki gurfanar a gaban kwamitin ladabtarwan jam'iyyar bayan ba shi wa'adin awanni 24.
Sanarwar ta ce kwamitin ya bukaci dan Majalisar ya gurfana a gabansa tun a ranar 26 ga watan Agusta amma ya ki mutunta gayyatar.
"Mun gayyace shi amma bai halarta ba kuma ba mu ji komai daga gare shi ko ofishinsa ba."
"Saboda haka jam'iyyar ta zargi Sewunmi da yi mata zagon kasa da kuma kin bin tsarin jam'iyyar a yankin Ojo."
- Jam'iyyar LP
Sauran matsalolin da 'dan majalisar ke ciki
Voice of Nigeria ta tabbatar da cewa jam'iyyar na zargin Sowunmi da kin halartar tarukanta na gunduma da ake gudanarwa.
Wasu gundumomi biyu a mazabarsa sun tabbatar a cikin wata wasika cewa babu sunan Sowunmi a jerin wadanda suka yi rijista a jam'iyyar.
LP ta rasa ikon Majalisar jihar Abia
A wani labarin, kun ji cewa jam'iyyar LP mai mulkin jihar Abia ta shiga damuwa bayan kwace ikon Majalisa ta PDP ta yi.
Jam'iyyar PDP ta yi nasarar kwace ikon Majalisar jihar bayan rantsar da Aaron Uzordike a jiya Talata 13 ga watan Agustan 2024.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng