“Dattijon Arziki Ne”: Shekarau Ya Fadi Wanda Ya Ba Shi Bashin Kudi a Takarar Gwamna

“Dattijon Arziki Ne”: Shekarau Ya Fadi Wanda Ya Ba Shi Bashin Kudi a Takarar Gwamna

  • Tsohon gwamnan jihar Kano, Ibrahim Shekarau ya koka kan halin rashin kudi da ya fuskanta lokacin takarar gwamna a 2003
  • Shekarau ya ce a lokacin jam'iyyar APP ta sanya kudin siyan fom na takara N5m amma ko N500,000 ba shi da su a lokacin
  • Sanatan ya ce marigayi Malam Magaji Danbatta ne ya taimaka masa da bashin N1m tare da samun N1.5m daga abokansa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Tsohon gwamnan Kano, Mallam Ibrahim Shekarau ya fadi irin kalubalen da ya fuskanta a siyasa.

Shekarau ya ce a zaben gwamnan Kano a 2003 sai da ya nemi bashin kudi domin siyan fom din takara kan N5m.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta gwangwaje 'yan Najeriya da tallafin N1.8bn a jihohi 36

Shekarau ya fadi yadda dattijo a Kano ya taimake shi da bashin kudin takara
Mallam Ibrahim Shekaru ya fadi yadda ya ci bashin kudin takara a zaben 2003 a Kano. Hoto: Mallam Ibrahim Shekarau.
Asali: Facebook

Yadda dattijo ya taimaki Shekarau a zabe

Tsohon gwamnan ya ce marigayi kuma dattijo, Mallam Magaji Danbatta ne ya taimaka masa da bashin N1m, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shekarau ya bayyana haka ne yayin taron lakca na tunawa da marigayi Danbatta inda ya ce ba zai taba mantawa ba.

Sanatan ya tuna yadda abokansa suka tara masa N1.5m domin neman takarar gwamnan jihar a 2003.

Yadda Shekarau ya ci bashin kudi a zabe

"A 2003, jamiyyar APP ta sanya N5m a matsayin kudin siyan fom na takarar gwamna, ni kuma ko N500,000 bani da shi amma abokin takara na Ibrahim attajiri ne mun samu labarin har ya sayi fom din a lokacin."
"Na je wurin marigayi Malam Magaji Danbatta na koka masa tare da neman taimakon bashin kudi, inda ya bukaci na rubuta ya kuma umarci daraktan Kano Forum ya bani kudin."

Kara karanta wannan

"Zan tsaya da kafafuna": Dan takarar gwamnan PDP ya sha alwashi, ya bugi kirji

"Lokacin abokaina sun hadamin N1.5m wanda hakan ya kama N2.5m amma duk da haka kudin ba su cika ba."

- Ibrahim Shekarau

Shekarau ya soki Ganduje kan siyasa

Kun ji cewa tsohon gwamnan Kano, Sanata Ibrahim Shekarau ya yi magana kan gayyatar da shugaban APC, Abdullahi Ganduje ya yi wa Gwamna Abba Kabir zuwa jam'iyyar.

Shekarau wanda tsohon sanata kuma tsohon Ministan ilimi ya bayyana gayyatar a matsayin matakin da bai kamata ba a cikin faifan bidiyo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.