Sunayen Gwamnonin Arewa da Ake Zargin Sun Kitsa Zanga Zangar Adawa da Tinubu, Rahoto

Sunayen Gwamnonin Arewa da Ake Zargin Sun Kitsa Zanga Zangar Adawa da Tinubu, Rahoto

  • Wani bincike na baya bayan nan ya fallasa wasu manyan 'yan siyasa da ake zargin suna yiwa gwamnatin Shugaba Tinubu bi ta da kulli
  • Rahoton da kungiyar ICDGN ta gudanar, ya nuna cewa gwamnan Kano da na Zamfara ne suka shirya zanga-zangar da aka yi a fadin kasar
  • Bayan binciken, kungiyar ta bukaci Shugaba Tinubu da ya duba bukatun masu zanga-zangar domin kaucewa faruwar hakan a nan gaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Wani rahoto mai zaman kansa na baya-bayan nan ya tuhumi Gwamna Dauda Lawal da Abba Kabir Yusuf a matsayin wadanda suka dauki nauyin zanga-zangar da aka yi a fadin kasar.

Rahoton ya yi Allah wadai da irin rawar da gwamnonin na Kano da Zamfara suka taka wajen mayar da zanga-zangar zuwa tashin hankali da barnata dukiyar jama'a.

Kara karanta wannan

Zargin rashin Turanci: An garkame hadimin Sanata Tambuwal kan sukar gwamna

Rahoto ya bayyana sunayen gwamnoni biyu da ake zargi da haddasa zanga-zanga a fadin kasar.
Ana zargin Gwamna Daudal Lawal da Abba Kabir Yusuf na da alaka da zanga-zangar da aka yi a fadin kasar. Hoto: @daudalawal_, @Kyusufabba
Asali: Twitter

Ana zargin wasu gwamnonin Arewa

BOARDROOM TV ta wallafa bidiyon rahoton da kungiyar ta fitar shafinta na Youtube a yayin da shugabannin ICDGN suka shirya taron manema labarai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton wanda Dakta Ben Omale Amodu, shugaban kungiyar kungiyar ICDGN ya karanta, ya bayyana irin yadda aka yi amfani da ‘yan daban siyasa domin tayar da zaune tsaye saboda cimma wata manufa.

Rahoton ya ce gwamnonin jihohin Zamfara da Kano da suka fito daga jam’iyyun adawa na PDP da kuma NNPP sun hada kan ‘yan bangar siyasa, suna tafka barna da satar dukiyoyin jama’a.

Inda binciken ICDGN ya karkata

Rahoton ya yi magana ne kan yadda aka lalata sakatariyar APC a jihar Zamfara, da kuma yunkurin kona gidan tsohon gwamnan jihar Zamfara.

Haka kuma, rahoton ya yi magan kan lalatawa da kuma kona babbar cibiyar masana'antu ta hukumar sadarwa ta Najeriya NCC da aka yi a jihar Kano, inji jaridar Daily Times.

Kara karanta wannan

Mafi karancin albashi: Gwamnatin Kano ta yi magana kan shirinta, akwai gyare gyare

Sakamakon rahoton ya nuna cewa wasu bata gari ne suka kwace zanga-zangar da aka fara ta matsayin nuna rashin gamsuwa da manufofin tattalin arziki na gwamnati.

ICDGN ta ba Tinubu shawara

An dai yi Allah wadai da matakin da ake zargin gwamnonin Zamfara da Kano suka dauka a na yin amfani da tashin hankula domin cimma wata manufa ta siyasa.

Kungiyar mai zaman kanta ta 'Coalition for Democratic Governance' ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta dauki kwakkwaran mataki don biyan bukatun masu zanga-zangar.

Ta ce daukar matakin zai hana afkuwar irin wannan zanga-zangar a nan gaba, da kuma hukunta wadanda ke da hannu a tayar da hankaluna da barnata dukiya.

Kalli taron kungiyar a nan kasa:

An nemi gwamna ya yi murabus

A wani labarin, mun ruwaito cewa hadimin tsohon gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, Kwamred Abdullahi Kaura ya nemi Gwamna Dauda Lawal da ya yi murabus.

Kwamared Kaura ya bukaci gwamnan na Zamfara da ya yi murabus idan har ba zai iya magance matsalolin jihar ba musamman abin da ya shafi tsaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.