Jigon PDP Ya Fadi Abin da Zai Sanya Atiku Ya Gaza da Ya Ci Zaben 2023
- Tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa, Cif Olabode George, ya yi magana kan abubuwan da suka shafi jam'iyyar
- Olabode ya bayyana cewa rikicin PDP ya samo asali ne sakamakon tsayar da Atiku a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023
- Ya bayyana cewa da Atiku ya ci zaɓen, da bai taɓuka komai ba domin mutanen ƙasar nan ba za su aminta da shi ba
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa, Cif Olabode George, ya yi magana kan Alhaji Atiku Abubakar.
Bode George ya bayyana cewa akwai yiwuwar da Atiku Abubakar ya lashe zaɓen 2023, ba zai taɓuka wani abin kirki ba a ƙasar nan.
Jigon na jam'iyyar PDP ya bayyana hakan ne a yayin wata tattauna da tashar talabijin ta Arise Tv a ranar Juma'a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me jigon PDP ya ce kan Atiku?
Jaridar The Nation wacce ta bibiyi tattaunawar ta ce ya bayyana cewa da Atiku ya lashe zaɓen shugaban kasa na 2023, da ya haifarwa da ƙasar nan matsaloli masu ɗumɓin yawa ciki har da kawo rashin tabbas a siyasar ƙasar nan.
Bode George ya nuna cewa idan da Atiku ya ci zaɓen da bai yi nasara ba a matsayin shugaban ƙasan Najeriya.
Jigon na PDP ya bayyana cewa rikicin da PDP take fama da shi a yanzu, ya samo asali ne saboda tsayar da Atiku a matsayin ɗan takarar jam'iyyar yayin da take da shugaba wanda ya fito daga Arewacin Najeriya, Iyorchia Ayu.
"Da Atiku ya yi nasara, da na zauna a gidana domin na san a nan gaba zai gaza. Ƙasar nan ba za ta taɓa yarda da shi ba."
"Idan da ya ci wannan zaɓen kana ganin ƙasar nan za ta zauna lafiya? Domin kuwa wani ɗan Arewa ya kammala shekara takwas, kuma ƙa’idarmu ita ce, bayan shekara takwas, ɗan takarar shugaban ƙasa zai fito ne daga Kudu."
"Waɗanda suke zagayawa domin neman muƙamai muna musu fatan Alheri."
- Atiku Abubakar
Atiku ya caccaki Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya sake caccakar gwamnatin APC ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu.
Atiku ya ce idan har yanzu APC ba ta gane irin wahalhalun da ƴan Najeriya ke ciki ba, hakan na nufin tun farko ba ta shirya yin mulkin ƙasar nan ba.
Asali: Legit.ng