2027: PDP Ta Kada Hantar Tinubu da APC, Ta Fadi Shirinta Na Dawowa Mulki
- Yayin daake tunkarar zaben 2027 a Najeriya, jam'iyyar adawa ta PDP ta sha alwashin kwace mulki daga APC a kasar saboda salon mulkinta
- Gwamnonin jam'iyyar PDP a Najeriya su suka yi sha alwashin inda suka caccaki salon mulkin Shugaba Bola Tinubu da jam'iyyarsa ta APC
- Shugaban gwamnonin, Sanata Bala Mohammed ya bayyana tsare-tsaren PDP domin tabbatar da inganta tattalin arziki da dakile matsalolin kasar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Taraba - Jamiyyar PDP a Najeriya ta shirya kwace mulkin Najeriya a zaben 2027 da muke tunkara.
Gwamnonin jam'iyyar ne a Najeriya suka bayyana haka inda suka caccaki tsarin mulkin jam'iyyar APC.
PDP ta sha alwashin kwace mulkin APC
Shugaban gwamnonin PDP a Najeriya, Sanata Bala Mohammed na jihar Bauchi shi ya bayyana haka a Jalingo na jihar Taraba a jiya Juma'a 23 ga watan Agustan 2024 cewar TheCable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan ya ce mulkin APC ya zama bala'i a Najeriya wanda hakan ya jefa al'umma cikin mawuyacin hali.
Sanata Bala ya bayyana himmatuwar jam'iyyarsu wurin tabbatar da inganta tattalin arzikin kasar, Tribune ta tattaro.
PDP ta yi alkawarin dakile matsalolin Najeriya
Ya ce jam'iyyar PDP ta shirya tsaf domin kawo karshen matsalolin Najeriya baki daya cikin kankanin lokaci.
Har ila yau, Sanata Bala ya koka kan yadda APC ta wargaza duka abubuwan cigaba da PDP ta samar a cikin shekaru 16 na mulkinta.
Jam'iyyar PDP ta bukaci gwamnonin jihohi da su yi amfani da tsare-tsarenta a jihohinsu domin samun yardar al'ummar da suke mulka saboda samun nasara a zabe.
Tallafi: Gwamnoni PDP sun gargadi Tinubu
A wani labarin, kun ji cewa gwamnonin jam'iyyar PDP a Najeriya sun caccaki Shugaba Bola Tinubu kan tallafi da ya ba jihohin kasar 36.
Gwamnonin sun koka kan yadda ake yada maganganun karya kan tallafin Gwamnatin Tarayya wanda ba zai wadatar da jihohin ba.
Wannan na zuwa ne bayan tallafin tireloli 20 ga jihohin Najeriya 36 da Gwamnatin Tarayya ta bayar domin rage radadin halin kunci.
Asali: Legit.ng