Dan Majalisar APC Ya Shiga Matsala, Jama'a Sun Fara Shirin Yi Masa Kiranye

Dan Majalisar APC Ya Shiga Matsala, Jama'a Sun Fara Shirin Yi Masa Kiranye

  • Mutanen mazaɓar Ondo ta Gabas/Ondo ta Yamma sun zargi ɗan majalisarsu, Abiola Makinde, da yin watsi da aikinsa na majalisa
  • Ganin ya tare a kasar waje suka yanke shawarar fara shirin yiwa ɗan majalisar wakilan kiranye domin sun gaji da rashin wakilcin
  • Sun ƙara da cewa mazaɓar ta shafe watanni ba ta da wakilci, yayin da ɗan majalisar ya samu waje ya yi zamansa a ƙasar waje

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Ondo - Ƙungiyar Ekimogun Roundtable ta ƴan asalin jihar Ondo ta fara shirin yin kiranye ga Abiola Makinde, ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Ondo Gabas/Ondo ta Yamma a majalisar wakilai.

Kungiyar ta yi zargin cewa ɗan majalisar na jam'iyyar APC ya yi watsi da aikinsa na majalisa ya koma ƙasar waje.

Kara karanta wannan

"Ana yi mani barazana": Ministan Tinubu ya koka kan kalubalen da yake fuskanta

An fara shirin yiwa dan majalisar APC kiranye
Ana shirin dawo da Abiola Makinde gida daga majalisa Hoto: Abiola Makinde
Asali: Facebook

Ƙungiyar na zargin ɗan majalisar na jam’iyyar APC da rashin gudanar da aikinsa na wakiltar al'ummar mazaɓar, cewar rahoton jaridar TheCable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa za a yiwa ɗan majalisar kiranye?

Muƙaddashin sakatariyar ƙungiyar, Christiana Ayodele, ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar, inda ta ƙara da cewa mazabar ta shafe watanni ba ta da wakilci a majalisa.

Christiana Ayodele ta bayyana cewa fiye da lauyoyi 30 a fadin ƙasar nan sun nuna sha'awar wakiltar su kyauta domin jagorantar dawo da ɗan majalisar gida daga majalisa, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.

"Ɗan majalisar ya sa ƙafa ya tsallake ayyukan da suka rataya a wuyansa na majalisa na tsawon watanni inda ya koma ƙasar waje da zama.
"Ko da yaushe ofishinsa na majalisa a kulle yake wanda hakan ya sanya gaba ɗaya mazaɓar ba ta da wakilci a tsawon wannan lokaci."

Kara karanta wannan

Dan takarar PDP ya sha kashi a zaben kananan hukumomin jihar Bauchi

- Christiana Ayodele

An fara shirin kiranye ga ɗan majalisar APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa mutanen mazaɓar Kaura Namoda/Birnin Magaji a jihar Zamfara sun fara shirin kiranye kan ɗan Majalisar wakilai a yankin, Aminu Sani Jaji.

Jama'ar yankin suka ce sun yi nadamar zaɓen Aminu Sani Jaji shiyasa suke kokarin daukar wannan mataki na dawo da shi gida daga majalisa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng