Awanni da Fallasa Badakalar Ganduje, ‘Dan Bello Ya Koma kan Gwamna Abba Gida Gida
- Bello Habib Galadanci ya yi sabon bidiyo da ya yi zargin gwamnatin Kano ta sabawa ka’idojin bada kwangiloli
- Ana tuhumar wani kamfani da samun kusan Naira biliyan 8 a shekara ta hanyar raba magunaguna a asibitocin Kano
- Dan Bello ya waiwayi gwamnatin NNPP ne bayan a baya ya taso tsohuwar gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Kano - Bello Habib Galadanci watau Dan Bello ya fitar da sabon bidiyo inda aka ga ya jawowa gwamnatin jihar Kano zargin badakala.
Kwanakin kadan bayan ya yi bidiyo yana zargin Murtala Sule Garo da Hafsah Ganduje, Dan Bello ya koma kan gwamnati mai-ci.
Novomed: Dan Bello ya tono rashin gaskiya?
A wannan bidiyo da ya zagaya shafin Facebook, Bello Habib Galadanci, ya yi zargin an ba da kwangila ba tare da an bi ka’idoji ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bidiyon Dan Bello yana tuhumar gwamnatin Abba Kabir Yusuf da karbar Naira miliyan 10 a hannun kowace karamar hukuma.
Daga wadannan makudan miliyoyi ake biyan wani kamfani kudi a duk wata da nufin samar da magunguna a asibitocin jihar Kano.
Dan Bello ya matasawa masu mulkin Najeriya
Da aka yi hira da shi a shirin siyasa na Daily Politics a tashar Trust TV, Dan Bello ya bayyana abin da ya sa yake tonon sililin nan.
A hirar ne aka ji yana cewa manufofin gwamnatin tarayya ba su aiki, ya soki yadda ake raba abinci da sunan kawar da talauci.
Matashin dai ya ce zai so so a kai shi kotu saboda yadda yake fallasa masu mulki, ya ce hakan ya nuna tasirin bidiyoyin da yake yi.
Bidiyon Dan Bello ya bi ta kan Kwankwaso
Tsohon ‘dan jaridar ya nuna wannan kamfani mai suna Novamed mallakar wani ‘dan uwan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ne.
Gwamnatin NNPP ta maido tsarin rabawa marasa lafiya magunguna kyauta a asibitoci.
Dan Bello ya bata sunan gwamnatin Kano
Idan ikirarin ya tabbata, kamfanin na kusa da tsohon gwamnan Kano kuma uban gidan Abba Kabir Yusuf yake cin moriyar tsarin.
Watakila wadannan miliyoyi da ake biyan kamfanin ya sabawa doka domin ba a cika sharudan ba da kwangiloli a gwamnati ba.
Ana so gwamnan Kano ya kori Sagagi
Kafin nan, rahoto ya gabata cewa ana zuga gwamna Abba Kabir Yusuf ya kori shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin Kano.
Dr. Abdulaziz Bako yana so Abba Gida Gida ya dakatar da Shehu Wada Sagagi saboda zargin da ake yi masa na karkatar da tallafi.
Asali: Legit.ng