Ana Fargabar Kitsa Makarkashiya ga Shirin Tazarcen Shugaba Tinubu a Zaben 2027

Ana Fargabar Kitsa Makarkashiya ga Shirin Tazarcen Shugaba Tinubu a Zaben 2027

  • Barakar da ta kunno kai jam'iyyar APC na shirin shafe kokarin da wasu ke yi na shugaba Bola Tinubu sake takarar shugaban kasa a 2027
  • Wannan na zuwa bayan kotu ta wargaza shugabancin riko na jam'iyyar a jihar Ribas, inda aka mayar da Emeka Beke a matsayin shugaba
  • Amma a taron ranar Alhamis, kwamitin gudanarwar jam'iyyar ya jaddada matsayar na cewa Tony Okocha kawai su ka dauka shugaba

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Rivers - Shugabancin riko na jam'iyyar APC a jihar Ribas ta bayyana wani hadadden shiri wasu 'yan jam'iyya na dakile takarar shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2027.

Kara karanta wannan

Jihar Kudu ta nemi daukin shugaban APC Ganduje domin ceto siyasar Tinubu a 2027

Wasu daga cikin yan APC na kokarin fara shirin tsayar da Tinubu takara duk da cewa bai cika shekara biyu a karagar mulki ba, kuma ana fama da tarin matsalolin tattalin arziki.

Tinubu
Ana fargabar dakile takarar Tinubu a 2027 a Ribas Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta tattaro shugaban riko na APC a Ribas, Tony Okocha ya ce sun gano wasu na shirin mayar da jam'iyyar 'yar amshin shatan gwamnatin jihar da hamayya ke mulki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu: An samu baraka a jam'iyyar APC

An samu rikicin cikin gida a jam'iyyar APC reshen jihar Ribas, wanda ya kai ga wani tsagin ya garzaya kotu domin ruguje shugabancin riko karkashin Tony Okocha.

Tsagin Emeka Beke ya yi nasara, inda aka nada shi shugaban jam'iyya, amma kwamitin gudanarwar APC ya yi watsi da hukuncin, tare da mubaya'a ga Tony Okocha.

Shugaban riko, Tony Okocha ya zargi Beke da jagorantar wadanda su ka zabi Rotimi Amaechi maimakon Tinubu ya tsaya masu takarar shugaban kasa a baya

Kara karanta wannan

Gwamna ya tattago aikin gina titi, ya toshe hanyar shiga sakatariyar APC ana shirin taro

An nemi tallafin Ganduje kan takarar Tinubu

A baya kun ji cewa masu kishin Jam'iyyar APC a jihar Enugu sun koka kan kokarin wasu daga cikinsu na dakile takarar shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2027.

Kungiyar ta nemi agajin shugaban jam'iyya, Dr. Abdullahi Umar Ganduje domin bankado masu shirin cin amanar APC da tabbatar da nasarar Tinubu a zaben gaba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.