Ana Shagalin Sallah, Bola Tinubu Ya Fara Samun Goyon Bayan Sake Neman Takara a 2027

Ana Shagalin Sallah, Bola Tinubu Ya Fara Samun Goyon Bayan Sake Neman Takara a 2027

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya fara samun goyon baya daga shugabannin siyasa gabanin babban zaɓen 2027
  • Jagororin jam'iyyar APC a shiyyar Kudu maso Kudu sun bukaci Tinubu ya sake neman takara karo na biyu a zaɓe mai zuwa
  • A cewarsu, sun aminta da salon shugabanci da tsare-tsaren da gwamnatinsa ta zo da su da nufin farfaɗo da tattalin arzikin Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Cross River - Jam’iyyar APC ta yankin Kudu-maso-Kudu ta yi kira ga shugaban kasa Bola Tinubu ya sake tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2027.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwar hadin gwiwa da shugabannin APC na Kudu maso Kudu suka fitar bayan wani taro da suka yi a Kalaba, jihar Kuros Riba ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Gwamna ya yi martani yayin da sojoji suka hallaka shugaban 'yan bindiga

Bola Ahmed Tinubu.
APC reshen Kudu masu Kudu ta amince Tinubu ya yi tazarce a 2027 Hoto: Dolusegun
Asali: Facebook

An fara goyon bayan tazarcen Bola Tinubu

Sun yabawa shugaban ƙasar bisa tsare-tsare, ayyuka da shirye-shiryen da ya zo da su bayan hawansa mulki, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsu, waɗannan tsare-tsaren tattalin arziki da Bola Tinubu ya ɗauka za su mayar da ƙasar nan kan turba mai kyau.

Shugabannin sun kara jaddada goyon bayansu ga tsare-tsaren Gwamnatin Tinubu a ɓangarorin shugabanci, tattalin arziki, tsaron ƙasa da ayyukan more rayuwa.

Yadda Tinubu ya fara mulkin Najeriya

A ranar 29 ga watan Mayun 2023, Tinubu ya ayyana kawo karshen tallafin man fetur, matakin da ya kawo hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya zuwa kashi 33.95 a watan.

Bayanai sun nuna cewa a rahoton shekara-shekara, hauhawar farashin kayayyaki ya ƙaru da kashi 11.54% idan aka kwatanta da na watan Mayun 2023 a kashi 22.41%.

Kara karanta wannan

"Ba faɗuwa na yi ba" Bola Tinubu ya yi magana kan abin da ya faru a Eagle Square

Amma duk da haka shugabannin APC na shiyyar Kudu maso Kudu sun yabawa shugaban kasa bisa jajircewa kan aikin hanyar gabar teku, da kuma fara aikin ta kowane ɓangare.

Bugu da ƙari, sun kaɗa ƙuri'ar amincewa da shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio a matsayin jagoran APC a shiyyar Kudu maso Kudu, The Sun ta ruwaito.

Gwamnatin Tinubu ta kare kanta

Kun ji cewa Gwamnatin tarayya ta yi martani ga labarin da wata jarida a kasar waje ta wallafa na cewa kasar nan na fuskantar mafi munin tabarbarwar tattalin arziki a tarihinta.

Hadimin shugaba Bola Ahmed Tinubu kan kafafen yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga ya dora laifin matsalolin da ake fuskanta kan gwamnatocin baya da gwamnatinsu ta gada.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262