“Idan Aka Zabe Ni”: Dan Takarar Gwamnan APC Ya Fadi babban Aikin da Zai Yi a Kwana 100

“Idan Aka Zabe Ni”: Dan Takarar Gwamnan APC Ya Fadi babban Aikin da Zai Yi a Kwana 100

  • Ana saura mako biyar a gudanar da zabe, dan takarar gwamnan APC ya dauki alkawarin samawa matasa 5,000 ayyukan yi idan ya ci zabe
  • A ranar 21 ga Satumba ne hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta shirya gudanar da zaben jihar Edo, wanda aka dade ana jira
  • Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Adams Oshiomhole, ya bukaci mazauna jihar Edo da kada su barnatar da kuri’unsu ga PDP

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Edo - Dan takarar gwamnan APC a jihar Edo, Sanata Monday Okpebholo, ya yi alkawarin samar da ayyukan yi ga matasa sama da 5,000 a cikin kwanaki 100 na farko na mulki.

Kara karanta wannan

Gwamna ya tattago aikin gina titi, ya toshe hanyar shiga sakatariyar APC ana shirin taro

Ya kuma ba da tabbacin samar da yanayi na zaman lafiya a Edo idan har ya ci zaben gwamnan jihar da za a gudanar ranar 21 ga watan Satumba, 2024.

Dan takarar APC ya yi magana kan samawa mutane 5,000 aiki idan ya ci zaben Edo
Edo: Dan takarar APC ya daukarwa matasa 5,000 alkawarin samun aiki a kwanaki 100 na mulkinsa. Hoto: @m_akpakomiza
Asali: Twitter

Okpebholo yayi magana ne a Auchi, hedikwatar karamar hukumar Etsako ta Yamma, yayin taron gangamin sanatan Edo ta Arewa na jam’iyyar APC, inji rahoton The Sun.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

APC ta nemi hadin kan mutanen Edo

'Dan takarar na babbar jam’iyyar adawa a Edo ya kuma yi alkawarin tabbatar da kyakkyawan shugabanci da ciyar da Edo gaba.

Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Adams Oshiomhole, ya bukaci mazauna jihar Edo da kada su barnatar da kuri’unsu ga PDP, amma su kada kuri’a ga APC.

Ministan raya Neja-Delta, Abubakar Momoh, wanda ya fito daga gundumar Edo ta Arewa, ya bukaci mazauna yankin da su tuhumi Gwamna Godwin Obaseki.

Kara karanta wannan

"Bakin jinin APC zai shafe ku": Dan takarar NNPP ya soki masu komawa jam'iyyar

The Nation ta ruwaito ministan ya yi ikirarin cewa gwamnan ya yi sama da fadi da shinkafar da gwamnatin tarayya ta turawa jihohi domin su rabawa talakawansu.

PDP ta bijirewa kotu kan dan takara

A wani labarin, mun ruwaito cewa jam'iyyar PDP ta yi kunnen uwar shegu da umarni wata babbar kotun tarayya da ta soke zabenta na fitar da dan takarar gwamnan Edo.

Jam'iyyar PDP ta dage kan cewa Asue Ighodalo shi ne zai ci gaba da kasancewa dan takararta na gwamnan Edo duk da kotun ta soke zaben fidda gwanin da ya samar da shi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.